August 13, 2021

Chelsea Ta Lashe Kofin UEFA Super Cup A Karo Na Biyu

Daga Baba Abdulƙadir 
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa Chelsea ta lashe kofin UEFA Super Cup bayan doke Villarreal da kwallaye 6-5 a matakin bugun fanareti yayin wasan da suka fafata daren Laraba da ta gabata, a filin wasa na Windsor Park da ke kudancin Belfast da ke  babban birnin yankin arewacin Ireland.
Kafin bugun faneretin din dai Chelsea ita ce ta soma jefa kwallo a ragar Villareal, inda itama ta rama daga bisani, aka kuma tashi wasa kunnen doki 1-1 bayan mintuna 90, da kuma karin wasu mintunan 30.
Dan wasan Hakim Ziyech ne ya fara zura kwallo a  mintuna 45 na farko, yayin da Gerard Moreno ya ramawa Villareal a mintuna na 73.
Wannan dai shi ne karo na biyu da Chelsea ke lashe kofin gasar UEFA Super Cup, tun bayan wanda ta lashe a shekarar 1998.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Chelsea Ta Lashe Kofin UEFA Super Cup A Karo Na Biyu”