February 19, 2023

Chanjin Kudi: Yadda Matata mai juna biyu ta rasa rayuwarta a Asibiti -Magidanci

Wata mata yar shekara 32 a duniya mai sun Shema’u Labaran ta rasa rayuwarta tare da juna biyu na tsahon watanni 9 a asibitin kwararru na Abdullahi Wase da ke a birnin Kano.

Rahotanni sun nuna cewa ta rasa rayuwarta ne sabida kasa biyan kudin aikin Asibiti da mai gidanta ya yi da sabbin kudi a kan lokaci.

Rahotannin dai sun nuna cewa an bar matar cikin ciwo da firgici sama da sa’o’I 8 ba tare da bata kulawa ba a asibitin.

A yayin da mai gidanta ke nakalto yadda abun ya faru, Malam Baffa mai shekaru 42 ya bayyanawa yan jarida cewa matarsa ta raba rayuwarta sabid zuban jini da tayi ta fama da shi a yayinda yake bangaren magani don biyan kudin Asibiti ta hanyar taransfa.

Malam Baffa ya bayyana cewa ya bata tsahon sa’o’I yana jiran mai karban kudi don ya tabbatar da shigar kudin da yayi masa taransfa zuwa asusun bankin sa. A yadda ya bayyana, kudin ya kai kimanin 8,528 na magunguna sabida bankin ya hana karban tsohon kudi, ya kuma ce malaman asibitin sun dage kan cewa bazasu duba matar ba har sai ya basu shaidar biyan kudin da ya biya.

 

Ya kara da cewa da farko ya kawo tsaffin kudi kimanin 8,500 ga mai karbar kudin, sai dai kuma ya gayamasa cewa hukumar asibitin ta saka dokan hana karbar tsaffin kudi, sun kuma ce hanya daya itace ya biya ta hanyar taransfa.

 

©Rahoton Punch Newspaper.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Chanjin Kudi: Yadda Matata mai juna biyu ta rasa rayuwarta a Asibiti -Magidanci”