January 16, 2023

​Cana Ta Bukaci HKI Ta Dakatar Da Kai Hare-Hare A Yankunan Falasdinawa Da Ta Mamaye

 

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Cana ta bukaci gwamnatin HKI ta dakatar da kai hare-haren harzukawa a yankunan Falasdinawa da ta mamaye a yankin yamma da kogin Jordan .

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto Qin Gang kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Cana ya na fadar haka a birnin Alkahira a lokacinda yake halattar taron da kafafafen yada labarai da tokwaransa na kasar Masar.

A cikin yan watannin da suka gabata dai gwamnatin HKI ta zafafa kai hare-hare kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye, hare-haren da suka kai ga mutuwar falasdinawa da dama da kuma kama wasu.

MDD dai ta bada sanarwan cewa shekara ta 2022 da ta gabata ita ce shekaran da HKI ta fi kashe al-ummar Falasdinu tun shekaru 16 da suka gabata. Rahoton ya kara da cewa Falasdnawa 171 ne suka rasa rayukansu a yankin yamma da kogin Jordan kadai sannan wasu 90,000 suka ji rauni.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Cana Ta Bukaci HKI Ta Dakatar Da Kai Hare-Hare A Yankunan Falasdinawa Da Ta Mamaye”