April 24, 2023

Burtaniya Ta Sanyawa Dakarun IRGC Na Iran Sabbin Takunkuman Tattalin Arzik

 

Gwamnatin kasar Burtaniya ta kakabawa jami’an gwamnatin jumhuriyar musulunci ta Iran daga ciki har da kwamnadojojin dakarun kare juyin juya halin musulunci 4, a safiyar yau Litinin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sakatren harkokin wajen kasar Burtaniya James Cleverly yana cewa takunkuman wadanda suka hada da hana tafiya zuwa kasar Burtaniya da kuma kwace kadarori, sun hada da kwamandojin dakarun kare juyin juya halin musulunci guda hudu.

Cleverly ya kara da cewa gwamnatinsa da kawayenta ba zasu daina daukar matakai kan JMI ba kan abinda ya kira take hakkin bil’adama da ke faruwa a kasar.

Ya zuwa yanzu dai Burtaniya, Amurka da kasashen kungiyar tarayyar Turai sun dorawa jami’an gwamnatin kasar Iran takunkuman tattalin arziki masu yawa da sunan take hakkin bil’adama.

A nata bangaren gwamnatin JMI ta maida martani da takunkuman tattalin arziki irin nata a kan wadannan kasashen.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Burtaniya Ta Sanyawa Dakarun IRGC Na Iran Sabbin Takunkuman Tattalin Arzik”