January 22, 2023

Burkina Faso ta bukaci dakarun Faransa su fice daga kasar.

Burkina Faso ta bukaci dakarun Faransa su fice daga kasar.

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta umarci sojojin Faransa da ke jibge a kasar da su tattara nasu ya nasu su bar kasar cikin wata guda.

Wannan umarni da kasar ta bayar shine sabon al’amari da ke kara tabbatar da tabarbarewar alaka a tsakanin Burkina Faso da uwar goyonta Faransa, tun bayan juyin mulkin watan Satumban bara.

A cewar ma’aikatar watsa labaran Burkina Faso, gwamnatin sojin ta yi watsi da wata yarjejeniyar jibge sojojin Faransa a kasar da aka kula tsakanin kasashen biyu a 2018, inda kuma ta basu wa’adin wata guda su bar kasar.

Kamfanin dillancin Labaran Faransa ya ruwaito cewa ya zuwa yanzu dai babu wani martini game da wannan sabon Lamari daga Paris. RFI Hausa

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Burkina Faso ta bukaci dakarun Faransa su fice daga kasar.”