April 30, 2023

Burkina Faso: Adadin Wadanda Aka Kashe A Kisan Kiyashin kauyen Karma Ya Karu Zuwa 136

 

Wata kungiya mai rajin kare hakkin bil’adama a kasar ta Burkina Faso, ta ce adadin mutanen da aka kashe a kisan kiyashin kauyen Karma, ya kai 136. Daga cikin wannan adadin da akwai mata 50, kananan yara 21 da suka kunshi jarirai da ba su wuce wata daya da haihuwa ba.

Tun a ranar Lahadin makon da ya shude, an bayyana adadin mutanen da aka kashe a wannan kisan kiyashin da cewa ba su wuce 60 ba.

Kungiyar da take fada da halayyar kin hukunta masu laifi wacce ake kira da ( CISC) a takaice ta fadawa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa; maharan sun ware mutane kowane rukunin gidaje a wuri daya, sannan su ka bai wa masu sanye da kakin soja umarnin su bude musu wuta da kashe su baki daya.”

A ranar 20 ga watan Aprilu ma an kai wani harin a kusa da kauyukan da suke kusa da Karma, inda aka kashe mutane 6 a kauyen Dinguiri, sai kuma wasu mutane 2 a Mene. A kauyen Ouahigouya da Barka kuwa an kashe mutane uku.

Kungiyar ta bayyana cewa, shaidun ganin ido sun sanar da ita ce sojoji da su ka yi wannan kisan kiyashin sun zarge su da bai wa ‘yan ta’adda mafaka.

Kungiyar wacce shugabanta Dauda Diallo ya taba samun kyautar Nobel ta zaman lafiya ta yi tir da kisan kiyashin, tare da yin kira da hukunta wadanda su ka aikata laifin.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Burkina Faso: Adadin Wadanda Aka Kashe A Kisan Kiyashin kauyen Karma Ya Karu Zuwa 136”