September 8, 2021

Buhari Ya Taya Sarkin Suleja Murnar Cika Shekaru 80

Daga Isah Muhd


Shugan kasa Muhammadu Buhari ya taya sarkin Suleja Alhaji Mohammed Awwal Ibrahim murnar cikar sa shekaru 80 a duniya a yau Laraba 8 ga watan Satumba.

Mai magana da yawun shugaban kasar wato Femi Adesina ne ya fitar da sanarwar taya murnar, inda ya nuna farin ckinsa da sanyawar albarka ga Sarkin da kuma masarautar Suleja baki daya.

Cikin bayanin ya zayyano matakan da Sarkin ya taka zuwa yau, kama da matakin Laccara zuwa shigarsa harkar siyasa da zamansa zababben gwamna na farko a jahar Neja a shekarar 1979.

Buhari ya bayyana ayyukan kwarai na Sarkin a matsayin abin alfahari ga Suleja, jahar Neja da kuma kasar Najeriya baki daya.

Daga karshe yayi masa addua da fatan tsawo rayuwa tare da lafiya.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Buhari Ya Taya Sarkin Suleja Murnar Cika Shekaru 80”