October 19, 2021

Buhari ya karbi bakuncin shugaban Turkiyya

Daga Balarabe Idriss


Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan don ziyara ta kwanaki biyu wacce zata fara daga ranar Talata.

A wani bayani da ya fita daga mataimaki na musamman ga shugaban kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya bayyana cewa shugaba Erdogan zai samu rakiyar mai dakin sa Emine wanda zasu taso daga kasar Angola.

Garba Shehu ya bayyana cewa shuwagabannin kasashen guda biyu zasu mai da hankali kan wasu al’amura da suka shafi yarjejeniyar (MoUs) kana kuma zasu rattaba hannu.

Ya kara da cewa bayan tattaunar tasu wacce ta kasance a kebance (na mutane biyu), shugaban na Turkiyya zai kaddamar da wata cibiyar al’adun Turkiyya a garin Abuja, a bangare guda kuwa mai dakin Erdogan, Emine a tare da uwar gidan shugaba Buhari, Aisha Buhari zasu kaddamar da wata sabuwar makarantar Sakandire a Wuse.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Buhari ya karbi bakuncin shugaban Turkiyya”