September 8, 2021

Buhari Ya Gana Da Shuwagabannin Hukumomin Tsaro

Daga Musa Kukah

A jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin Hukumomin tsaro na Najeriya kan matsalar sace-sacen mutane da kashe kashe da yaki karewa a kasar musamman a yankunan Arewa ta tsakiya da Arewa maso yamma.
Shugaban ya nemi hukumomin tsaron da su ninka kokarin da suke wurin dawo da zaman lafiya a kasar da kuma bai wa yan Kasa karfin gwiwa da sabuwar fata na dawowa harkokin su kamar yadda suka saba.

Ya kuma kara da basu damammaki na su nemi sabbin hanyoyi da salo da zasu bi don kawo karshen matsalar tsaron musamman tunda ya samar musu da isassun malamai na zamani da zasu yi amfani dasu don aiwatar da hakan.
Ministan tsaro Bashir Magashi da Sufeto Jan at na yan sanda Usman Alkali Baba ne suka bayyana hakan bayan ganawar shuwagabannin Hukumomin tsaron da shugaba Buhari.
Sufeto Janar din ya bayyana cewa shugaba Buharin ya yaba musu bisa kwazon su wanda ya samar da sakamako mai kyau musamman a yankunan Arewa maso gabas da Kudu masu gabas.

Inda Sufeto janar din yace tabbas sun gana da shugaban Kasa inda suka zayyana masa halin da kasar ke ciki a yanayin tsaro sannan kuma shugaban yayi karin bayani cewa a samar da tsaro ga al’ummar Kasa na daga abu mafi muhimmanci da kundin tsarin mulkin kasa ya rataya a wuyan gwamnati sannan yana shirye ya sauke wannan nauyi dake rataye a wuyansa.

Ya kuma bayyana cewa daga karshe sun bai ma shugaban tabbaci ta hanyar alkawaranta masa cewa zasu ninka kokarin su da kuma zage damtse wurin kawo karshen yan bindigan da suka haifar da matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Buhari Ya Gana Da Shuwagabannin Hukumomin Tsaro”