October 30, 2021

Buhari ya dawo gida Nijeriya bayan halartar taro a kasar Saudiyya

Daga Balarabe Idriss


Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya dawo gida Nijeriya a jiya Juma’a inda ya sauka a filin jirgi na birnin Abuja daga birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

Shugaban ya ziyarci kasar ce don halartar wata taro wanda ta gudana bisa gayyatar da Sarki Salman bn Abdulaziz yayi masa, shugaban tare da mukarraben sa sun kuma gudanar da Umara bayan kammala taron, inda ya yi adduar nasara da kuma zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummar kasar.

Shugaba Buhari ya sauka a filin jirgi na Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja, inda ya samu tarba ta musamman daga wasu manyan mutane da suka hada da shugaban ma’aikatan sa, Farfesa Ibrahim Gambari, Ministan birnin tarayya Abuja, Malam Muhammad Musa Bello, Babban sufetan ‘yan sanda na kasa IGP Usman Alkali Baba da kuma shugaban ‘yan sanda na farin kaya Yusuf Magaji Bichi.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Buhari ya dawo gida Nijeriya bayan halartar taro a kasar Saudiyya”