November 23, 2021

Buhari – Hare-haren ‘yan bindiga na kara haifar da yaduwar talauci a Nijeriya

Daga Danjuma Makery


Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa hare-haren da yan bindiga ke yawan kaiwa a sassan kasar ta Nijeriya na haifar da ta’azzarar talauci da hijira a tsakanin al’ummar kasar.

Ya kuma nuna damuwar sa kan yadda zaman lafiya da lumana ya zama mawuyaci da kuma yadda hakan ke taka rawar gani wurin koma baya a sassa dayawa na nahiyar Afirka.

Ya gabatar da jawabin ne a birnin tarayyar Nijeriya Abuja jiya Litinin a yayin da yake bude taron da ya gudana na kan yunkurin wanzar da zaman lafiya Wanda matayen shuwagabannin kasashen Afirka suka gudanar a karo na 9.

Ya kuma yi kira ga shuwagabannin Afirka da ma sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin gudanarwa da su tallafawa mata wajen kokarin su na gina al’ummar da take da yalwar zaman lafiya.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin tallafawa kungiyar ta (AFLPM) wurin cimma burin su na Samar da wanzazziyar zaman lafiya da kuma cigaba a nahiyar ta Afirka.

Inda yace “Ba na tantamar cewa mata da kananan yara sune wadanda tabarbarewar lamarin zaman lafiya ya fi shafa, a saboda haka, Ina da imanin cewa ku ne kuka fi cancanta kuma kuka fi kasancewa a matsayin samar da al’ummar da ke cike da zaman lafiya”.

A karshe kuwa shugaba Buhari ya jinjina wa uwar gida Aisha Buhari kan kokarin da ta yi na samar da fili a madadin sauran matayen shuwagabannin Afirka don gina wata cibiyar kungiyar ta AFLPM a birnin Abuja.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Buhari – Hare-haren ‘yan bindiga na kara haifar da yaduwar talauci a Nijeriya”