October 6, 2021

Buhari ya gana da Jonathan a fadar gwamnati

Daga Balarabe Idriss


Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Ebele Jonathan yau Laraba a fadar gwamnati dake birnin tarayya Abuja, inda suka yi tattaunawa ta sirri.

Ya zuwa yanzu ba’a san dalilin ziyarar tsohon shugaban kasar ba a saboda bai gana da yan jaridu ba bayan fitowarsa.

Rahotanni sun nuna cewa Dr. Goodluck Jonathan ya kai ziyarar ne a yammacin yau Laraba da misalin karfe 4 na yamma.

Sai dai ana kyautata zaton tattaunawar na da alaka da matsalolin tsaro da ke addabar kasar da ma yankunan yammacin Afirka baki daya.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Buhari ya gana da Jonathan a fadar gwamnati”