November 19, 2021

Borno: Dakarun sojan Nijeriya sun yi gagarumar nasara kan mayakan Boko Haram a Damboa

Daga Muhammad Bakir Muhammad


 

Rahotannin da suke zuwa mana daga jihar Borno a yau jumu’a na nuna yadda mayakan Boko Haram suka kwashi kashin su a hannu a yayin arangamar su da dakarun sojan Nijeriya a karamar hukumar Damboa.

Gagarumin nasarar da dakarun sojan Nijeriyan sukay kan mayakan na Boko Haram ya haifar da sabuwar fata da farin ciki na musamman a zukatan mutanen da ke zaune a yankin.

Rahoton ya nuna cewa mayakan na Boko Haram sun kai farmaki da safiyar yau jumu’a da misalin karfe 6:35, inda suka bude wuta kan mazauna yankin.
Wannan farmakin ya haifar da tsoro da zaman dar a zukatan mutanen yankin, sai dai cikin ikon Allah ba tare da bata lokaci ba dakarun sojan Nijeriya suka kawo masu dauki, inda suka yi arangama mai zafin gaske tsakanin su da mayakan na Boko Haram, inda daga karshe sojojin suka fatattake su kana kuma suka tilasta musu gudu da fita daga yankin.

Wasu mazauna yankin sun shaidawa manema labarai cewa mayakan na Boko Haram basu kasance a yankin na sama da mintuna 30 ba.

Sai dai kuma rahoton ya tabbatar da cewa wasu daga mutanen kauyen da basu gaza mutane 8 ba a kauyen na Kala sun ji raunuka sakamakon harbin bindiga a yayin farmakin.

Ya zuwa yanzu babu sauran tashin hankali a yankin, kuma a bangare guda mazauna yankin sun nuna farin cikinsu kan kwazo da jarumta wanda dakarun sojan Nijeriya suka nuna.

 

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Borno: Dakarun sojan Nijeriya sun yi gagarumar nasara kan mayakan Boko Haram a Damboa”