January 23, 2023

Borell : EU Ba Zata Iya Yanke Shawarar Sanya Dakarun Iran A Jerin Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda

Borell : EU Ba Zata Iya Yanke Shawarar Sanya Dakarun Iran A Jerin Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda
Shugaban kula da manufofin ketare na kungiyar tarayyar turai Josep Borell, ya bayyana a wanann Litinin cewa mambobin kungiyar 27 basu kai ga iya daukar mataki ba na sanya dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran, a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya.
“Wani abu ne da ba za a iya yanke hukunci ba sai da kotu, Ana bukatar hukuncin kotu,” in ji Borrell.

Ba zamu iya daukar wani mataki ba, sai idan wata kasa ta gabatar da batun gaban kotu tare da hujjoji masu karfi, inji shi.

Kalamman na Mista Borell na zuwa ne kwana guda bayan da ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa, Akwai yiwuwar kasarsa ta fice daga yarjejeniyar hana yaduwar makamman nukiliya ta NPT idan har kungiyar Tarayyar Turai ba ta gyara matsayinta ba, kan sanay dakarun na IRGC a jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya.

Saidai ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai sun amince da sabbin takunkumai kan Iran a wannan Litinin, kamar yadda fadar shugaban kasar Sweden a EU ta sanar.

Matakin a cewar ministocin domin yin Allah wadai ne da abunda suka kira amfani da karfi kan masu zanga-zangar data barke bayan mutuwar matashiyar nan Mahsa Amini ‘yar shakara 22 a watan

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Borell : EU Ba Zata Iya Yanke Shawarar Sanya Dakarun Iran A Jerin Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda”