January 28, 2024

Bom Ya Kashe Mutane 6 a Gubion jihar Borno

Dayake amsa tambayoyin Manema labarai jiya asabat  a karamar hukumar Gubio Shugaban karamar hukumar  Mali Gubio, ya ce abun fashewan ya tashi ne a cikin wani kango da ke kusa da tsangayar almajiran a safiyar ranar Asabar dinnan.

An gano gawar kananan yara almajirai hudu da wasu manya biyu, amma har yanzu ba a kai ga gano ’yan uwansu ba

Saboda baka ba za mu iya fadin hakikanin abin da ya faru ba,

amma dai bam ya tashi a wani gida da ake ajiye kayan gwangwan

An gano gawar kananan yara almajirai hudu da wasu manya biyu, amma har yanzu ba a kai ga gano ’yan uwansu ba

“Dukkansu sun rasu, saboda baka ba za mu iya fadin hakikanin abin da ya faru ba, amma dai abun fashewa ya tashi a wani gida da ake ajiye kayan gwangwan,” in ji s hugaban karamar hukumar.

A cewarsa, wasu na zargin ’yan bola-jarin sun dauko abun fashewan bisa rashin sani ne suka hada da kayan da suka tara a kangon da ke kusa da tsangayar.

Shugaban karamar hukumar ya kuma jaddada umarnin Gwamna Babagana Umara Zulum, na haramta ayyukan ’yan bola-jari a jihar, da nufin hana sace-sace kayan gwamnati a wuraren da mutane suka kaurace wa.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Bom Ya Kashe Mutane 6 a Gubion jihar Borno”