May 23, 2024

Bikin tunawa da Shugaba Raisi da aka gudanar a Washington

An gudanar da bikin karrama shugaban kasar Shahadi Ibrahim Raisi da ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian a birnin Washington.

Kamfanin dillancin labaran Iran ya habarta cewa, an gudanar da bikin ne a cibiyar koyar da ilimin addinin musulunci ta birnin Washington DC, babban birnin kasar Amurka.

Iraniyawa da dama da ke zaune a Amurka, da kuma masu fafutukar kare Jumhuriyar Musulunci ta Iran da ba Iraniyawa ba, sun halarci bikin tunawa da ranar a birnin Washington.

Bayan karatun kur’ani mai tsarki da jinjinawa, shugaban ofishin kula da muradun Iran a birnin Washington, Mehdi Atefat, ya gabatar da jawabin tunawa da shahidan hidima a birnin Washington.

Jirgin sama mai saukar ungulu dauke da shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi da abokansa dake kan hanyarsa zuwa Tabriz, ya yi hatsari a dajin Dizmar dake tsakanin kauyukan Uzi da Pir Daoud.

Ebrahim Raisi, Hojjatul-Islam Ale-Hashem Limamin Sallar Juma’a na Tabriz, Hossein Amir-Abdollahian, Ministan Harkokin Waje, Malek Rahmati, Janar Gwamnan Azarbaijan ta Gabas, matukin jirgi, mataimakin matukin jirgi, babban ma’aikatan jirgin, shugaban tawagar tsaro na daya. na masu tsaro da wasu Abokai da dama ne a cikin jirgin kuma duk sun yi shahada tare da shugaban.

Fassaran,Hauwa Suleiman.

Daga,Press tv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Bikin tunawa da Shugaba Raisi da aka gudanar a Washington”