August 27, 2023

​Biden Ya Gayyaci Tinubu Domin Tattaunawa Kan Batun Nijar.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya mika goron gayyata ta musamman ga shugaban Najeriya Bola Tinubu domin tattauna batun takun sakar siyasa a jamhuriyar Nijar, a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da za a fara gudanar a watan Satumba mai kamawa.

A wata sanarwa da mai baiwa shugaba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce Biden yana bukatar yin magana da shugaban Najeriya kan yadda Najeriya za ta hada kai da Amurka wajen tallafawa domin ganin an warware dambarwar da ake fama da ita a Nijar.

Tinubu ya shaida wa tawagar Amurka cewa yaki a Nijar ba zai yi illa ga sauye-sauyen tattalin arzikin da ya ke yi ba, amma ya ba da tabbacin cewa za a dawo da dimokuradiyya a kasar ta hanyoyin diflomasiyya a Nijar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin gwamnatin kasar Faransa ke ta matsa lamba kan kungiyar ECOWAS domin ta dauki matakin soji a kan Jamhuriyar Nijar, da sunan neman dawo da hambararren shugaban kasar Muhammad Bazoum.

An samu rarrabuwar kai tsakanin kasashen ECOWAS kan batun daukar matakin soji a kan Nijar, yayin da wasu daga cikin kasashen na ECOWAs da suka hada da mali da Burkina Faso, suka sha alwashin taimaka ma Nijar, matukar dai aka kai mata harin soji.

 

®VoH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Biden Ya Gayyaci Tinubu Domin Tattaunawa Kan Batun Nijar.”