February 2, 2023

Bene mai hawa hudu ya rufta kan mutane a Abuja

Mutane da dama sun makale a karkashin buraguzan wani bene mai hawa hudu da ya rufta a Gwarinmpa da ke birnin Abuja na Najeriya a safiyar wannan Alhamis.

Kawo yanzu, babu cikakken bayani game da yadda wannan ibtila’in ya auku, amma wasu majiyoyi na cewa, an fara zakulo gawarwakin wasu da suka mutu a sanadiyar ruftawar benen.

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Abuja ta shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, kawo yanzu, ta yi nasarar ceto mutane 11,inda nan take aka garzaya da su babban asibitin Gwarinmpa.

Ko a cikin watan Agustan bara, wani bene mai hawa biyu ya rufta a Kubwa da ke Karamar Hukumar Bwari a birnin na Abuja, inda a wancan lokacin aka samu asarar rai guda.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Bene mai hawa hudu ya rufta kan mutane a Abuja”