December 12, 2023

BBC ta bankaɗo cocin da ke addu’o’in ‘cire aljanu’ a Birtaniya

An dauki hoton wani reshen cocin Kirista a Burtaniya a asirce yana kokarin korar aljanu daga wani yaro dan shekara 16.

 

An ga wani Fasto na Cocin Universal Church of the Kingdom of God (UCKG) yana karanta abin da ake kira “karfafan addu’o’i” don kawar da aljanu daga yaron.

 

Wani tsohon dan luwadi ya shaida wa BBC Panorama cewa an sha yi masa addu’o’i mai karfi tun yana ɗan shekara 13 don kokarin daidaita shi.

 

UCKG ta ce ba a barin ‘yan kasa da shekaru 18 su shiga wajen da ake yiadu’o’in masu ƙarfi don kawar da aljanu.

 

Wani bincike na BBC Panorama ya gano:

 

Iklisiya ta gaya wa ikilisiyoyinta cewa za ta iya taimakawa da yanayin lafiyar hankali ta hanyar korar aljanu.

 

Shugaban cocin a Burtaniya ya kwatanta ciwon farfadiya a matsayin “matsala da adu’o’i ke iya magancewa.”

 

UCKG tana da rassa a duniya, ciki har da 35 a Burtaniya, inda aka yi mata rajista a matsayin mai bayar da agaji.

 

Ta ce tana da mambobi sama da 10,000 a faɗin ƙasar kuma ta bayyana kanta a matsayin cocin Pentikostal na Kirista.

 

Addu’o’in fitar da aljanu ba sabon abu ba ne a duniyar Kirista. Wasu majami’u suna kiran Cocin UCKG na da rassa a faɗin duniya, ciki har da 35 a Birtaniya, inda take da rajista a matsayin gidauniya. Ta ce tana mambobi fiye da 10,000 a Birtaniyar kuma ta ayyana kanta a matsayin cocin ɗariƙar Pentecostal.

 

Addu’o’in cire aljanu ba sabon abu ba ne a addinin Kirista. Sai dai UNKG ba ta amfani da sunan da sauran Kiristoci ke kiran su.

 

Dr Joe Aldred, wani bishop na ɗariƙar Pentecostal da ke aikin haɗa kan mabiya ɗriƙun Kiristoci, ya ce: “Cocin Ingila na da sashen addu’o’in cire aljanu [exorcism] a rassanta sosai. Abin tambayar shi ne irin yadda suke yin nasu.”

 

“Addu’a mai ƙarfi” a UCKG na nufin fasto zai ɗora hannu a kan mamban coci kuma ya nemi shaiɗanin aljanin ya bar jikin mutum. Cocin ta ce tana gudanar da addu’o’in ne don “don tsarkake ruhi” duk mako “don magance tushen matsalar”.

 

UCKG ta fara fuskantar matsi ne bayan kisan wata yarinya mai shekara takwas Victoria Climbie, wadda wata gwaggonta da saurayinta suka azabtar har ta mutu.

 

Mako ɗaya kafin mutuwarta a 2000, mutanen biyu suka ɗauki Victoria – wadda ke nuna wa wata coci alamun cin zarafinta da ake yi.

 

Wani fasto ya ce yana ganin aljanu ne suka kama ta kuma ya bayar da shawarar a kai ta wurin addu’a inda “za a yi mata addu’o’i masu ƙrfi”. Daga baya, kafin a fara addu’o’in sai faston ya umarci matar ta kai Victoria asibiti.

 

Rahoton wani kwamiti ya ce “ba a kai rahoton cikakken halin da Victoria take ciki ba ga hukumomin da suka dace” kafin ta rasu.

 

Bayan wannan sukar, cocin ta ƙaddamar da wani tsari. Yanzu ta ci alwashin baza ta sake yi wa wani addu’a mai ƙarfi ba matuƙar bai kai shekara 18 ba – ko kuma a kan idonsu.

 

Shirin BBC Panorama ya kai ziyara wajen addu’o’in matasa na UCKG a Brixton da ke kudancin Landan, inda samari da ‘yan mata ke halarta.

 

Bidiyon da aka ɗauka a asirce ya nuna yadda faston ke ware matasan gwargwadon shekarunsu.

 

Wani yaro da ya faɗa wa shirin Panorama cewa shekararsa 16 a lokacin, an gan shi yana shan addu’o’in “masu ƙarfi” daga faston. “Allah ya sa wutar da ke jikinka ta ƙona shaiɗanin da ya ɓuya,” in ji faston.

 

BBC ta nuna wa Jahnine Davis bidiyon, wadda ke cikin wani kwamiti na kare haƙƙi mai zaman kansa.

 

Ta ce: “Ganin cewa mutuwar Victoria Climbie ta faru ne fiye da shekara 20 da suka wuce, ya kamata UCKG ta tambayi kanta darasin da ta koya musamman ganin bidiyon da kuka ɗauka.

 

“Matakin kare tsari wani abu ne daban amma ba su da wani amfani idan ba za a dinga aiwatar da su ba.”

 

Cikin wata sanarwa, UCKG ta ce: “Addu’o’i masu ƙarfi …ana gudanar da su ne a wuraren addu’a na musamman, kuma duk wanda bai kai shekara 19 ba ba za a bari ya shiga ba.

 

Ta musanta batun cewa ta karya tsarin nata na kare matakan bin tsari.

 

Cocin Universal Church of the Kingdom of God na iƙirarin cewa tana sauya rayuwar mabiyanta da ke da rassa sama da 30 a Birtaniya.

 

BBC Panorama ya yi magana da mutum 40 tsofaffin mambobin UCKG – wasu sun fice ne shekaru da yawa da suka wuce, wasu kuma ‘yan watanni da suka wuce.

 

Sharon ta shiga reshen Stratford ne lokacin da take shekara 19.

 

Ta ce ta faɗa wa wani fasto halin tsananin damuwa da take ciki amma bai taɓa ba ya shawarar neman taimakon likitoci ba.

 

Ta ce an saka ta a layin “addu’o’i masu ƙarfi” – abin da ya saɓa da tsarin UCKG, wanda ya ce bai kamata a yi wa mutanen da ke da lalurar ƙwaƙwalwa ba.

 

“Har sai da aka kai lokacin da na ji ina tsoron zuwa wuraren addu’ar saboda ni ake nema a kodayaushe,” in ji Sharon.

 

Yayin wani taron addu’a da BBC ta naɗa a asirce a inda ake gudanar da “addu’o’i masu ƙarfi”, Bishop James Marques – shugaban UCKG a Birtaniya – ya faɗa wa mabiya cewa wasu cutukan matsalar ruhi ce kuma lalurar ƙwaƙwalwa na da alaƙa da shaiɗanun aljanu.

 

Ya faɗa wa wani ɗan jarida da ya ɓatar da kama: “Cutar tsananin damuwa ta ruhi ce. Shaiɗanin aljani ne ke jawo ta.”

 

“Mun san cewa cutar farfaɗiya na buƙatar kulawar likitoci amma a littafin Linjila Yesu ya kori shaiɗanin da ke haddasa ta. Saboda haka za mu fahimci cewa farfaɗiya cuta ce da ke da alaƙa da ruhin mutum, wadda ke shafar zahirin jikin mutum.”

 

Cikin wata sanarwa, UCKG ta ce “addu’o’i masu ƙrfi” ba su taɓa zama madadin kulawar likitoci ba…ko kuma kulawar ƙwararru”.

 

Sharon ta ce an nuna mata wani bidiyo na wani tsohon mamban cocin wanda ya yi hatsari a kan babur kuma dukkan, inda ta ga “dukkan gaɓoɓinsa a waje”.

 

“Suka ce min abin da zai faru da duk wanda ya bar cocin ke nan, shaiɗan zai ƙwace ruhin mutum.”

 

UCKG ta faɗa wa BBC cewa “ba ta amfani da tsarin tsoratarwa”, ana yi ne kawai ga waɗanda suka amince” kuma “ba ta tilasta wa mutane”.

 

Cocin ta ce mambobinta na yanzu na godiya da ayyukanta da kuma abubuwan da take cimmawa.

 

Amma da yawa daga tsofaffin mambobinta da suka yi magana da BBC sun ce ba za su koma ba.

SHARE:
Tarbiyyan Yara 0 Replies to “BBC ta bankaɗo cocin da ke addu’o’in ‘cire aljanu’ a Birtaniya”