March 28, 2023

Bazamu lamunci duk wani yunkuri ba da zai iya haifar da barazana ga tsaron kasa,

A ranar litinin 27 ga wata Sefeto janar na `yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya jagoranci taron manyan jami`an `yan sandan kasar da suka hada da kwamashinoni domin nazartar irin rawar da `yan sanda suka taka yayin zabukan kasar da suka gabata.
Yayin taron wanda aka gudanar da shi a hedikwatar hukumar dake birnin Abuja, Sefeton `yan sandan na Najeriya yace rundunar zata dauki matakin ba sani ba sabo wajen hukunta duk masu kokarin haifar da fitina bayan sanar da sakamakon zabuka da aka yi.
Daga tarayyar Najeriya,
Ya ce taron ya zama wajibi bisa la`akari da yadda yanayin tsaron kasar ke fuskantar barazana daga wasu manyan `ya siyasa wadanda suke neman fakewa da sakamakon zabuka domin sukurkutar da kyakkyawan yanayin zaman lafiya da ake da shi a kasar.
“A don haka ina gargadin cewa rundunar `yan sanda ta kasa da sauran hukumomin tsaro baza su lamunci duk wani yunkuri ba da zai iya haifar da barazana ga tsaron kasa, a don haka muna shawartar wadannan `yan siyasa da su janye irin wannan yunkuri nasu domin kaucewa cin karo da fushin hukuma.”
Shugaban `yan sandan na Najeriya ya ce a yanzu haka rundunar da kuma hukumar zabe ta kasa suna kan aikin binciken dukkan rikicin da ya biyo bayan zabukan da suka gabata da kuma ta`addancin da aka aiwatar yayin zabukan a wasu yankuna na kasar.
Ya sanar da cewa `yan sanda sun samu nasarar kame mutane 781 bisa laifin karya dokokin zabe a yayin babban zaben na 2023.
Haka kuma ya ce an kame mutane 203 bisa hannu wajen cin zarafin jama`ar yayin zaben shugaban kasa.
A zaben gwamnoni da ya gabata kadai adadin laifukan karya dokokin zabe guda 304 aka samu sannan an kame mutane 578 da suka aikata laifin.
“A kan haka ne ma nake shawartar dukkan manyan jami`an `yan sandan da idan akwai mutanen da har yanzu suke a tsare da a sake su amma fa sai bayan sun gabatar da bayanan wadanda zasu tsaya masu kafin lokacin da za a zartar masu hukunci na shari`a.

©(Garba Abdullahi Bagwai)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Bazamu lamunci duk wani yunkuri ba da zai iya haifar da barazana ga tsaron kasa,”