September 18, 2021

Bayelsa: Masu Garkuwa Da Mutane Sun Raunata Yan Sanda Biyu Da Dan Banga Guda

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Wasu jami’an yan sanda biyu tare da wani Dan banga a unguwar Adgbabiri dake karamar hukumar Sagbama dake jahar Bayelsa a yau Asabat sun raunata a yayin kokarin su na kama wasu mutane da zargi masu garkuwa da mutane ne.

Mazauna unguwar sun bayyana cewa mutanen suna shirye shiryen yadda zasu sace wani mutum a unguwar da kuma yin garkuwa da shi a dalilin haka yan banga na unguwar suka sanar da yan sanda cikin gaggawa a yayin da suka kewaye mafakar masu garkuwa da mutanen.

Rahoto ya nuna cewa an samu nasarar cafke biyu daga cikin su a yayin da sauran suka tsere.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan jahar, SP Asinim Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya tabbatar da kama biyu daga cikin masu garkuwa da mutanen.
Inda ya bayyana sunan mutanen biyu, wanda daya daga cikin su ake kira Odulima Igbogiri Dan asalin Okogbie da kuma Moses Joshua dan asalin garin Ahoada wadanda dukkanin su yan asalin jahar Rivers ne.

 

Jami’in ya bayyana cewa biyu daga cikin jami’an su sun sami rauni a yayin kokarin kama mutanen kari da daya daga cikin yan banga na unguwar shima ya samu rauni a tare da yan sandan. Daga karshe ya bayyana cewa wadanda suka raunata an garzaya dasu zuwa babban asibitin Sagbama don yi musu magani, a bangare guda kuwa masu laifin suna amsa tambayoyi daga yan sanda.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Bayelsa: Masu Garkuwa Da Mutane Sun Raunata Yan Sanda Biyu Da Dan Banga Guda”