April 15, 2023

BAYAN LAILATUL ƘADRI, SAI KUMA ME.?

 

–Muminai sun raya waɗannan dararen na ƙadri masu tarin albarka (cikinsu akwai NI da KU) bisa ƙaddarawa da dacewa daga Allah ta’ala…

–Dukan mu mun yi ta kiran “YA UBANGIJINMU”. Mun kira shi da kyawawan sunayensa, kira da roƙo irin na neman taimako da agaji, mun zanta da shi (a sanyaye) irin yadda masoyi ke zantawa da masoyinsa, mun ruga izuwa gare shi da ayyukanmu mun yi fatan ya sauƙaƙa mana gajiya da wahalhalu…

–A waɗannan dararen ne dai muka sanya masu ceto a tsakaninmu da Ubangijinmu waɗanda Allah ta’ala ba ya ƙin yi domin su. Su ne; Alƙur’ani mai girma, Manzon rarahama (s) da Imaman hiriya (a), dan ya karɓe mu a matsayin masu dawowa da tuba zuwa gare shi… Ko ba haka ba?

TO BAYAN DUK WANNAN SAI KUMA ME?
–Haƙiƙa Raya dararen ƙadri suna a matsayin wasu abubuwa ne guda 2 masu muhimmanci:
1:– Daidaita hange (tunani da nazari) da kuma gyara mafiskanta, domin a lokutan addu’o’i mun gane cewa dukkan motsinmu dole ne ya zama ga Allah ne kuma domin shi… Domin kuwa komai me gushewa ne in banda shi, kuma kowace manufa ɓatacciya ce, in ba ta neman yardarsa ba ce…
2:– Shiga sabon shafi na (gayara da kyautata) alaƙa tsakanin mu da Allah ta’ala, da kuma rura wutar sanin Allah maɗaukaki da imani da shi…

BAYAN DARAREN ƘADRI:
–Dolen mu ne mu kiyaye wannan garwashin wuta (na sanin Allah) a wani waje (na musamman) a cikin zukatanmu. Mu dage wajen cigaba da rura wannan wuta har sai mun kai ga samun ɗimi daga gare ta, ta raru ta yadda za mu iya hankakuwa da ita a duk san da sheɗan ya sanya mana wani wasi-wasi, ko zuciyarmu ta tunkuɗa mu ga aikata wani saɓo…

–Sannan dolen mu kuma kada mu manta, cewa cigaba da wanzuwa a kan wannan garwashin wuta ba abu ne mai sauƙi ba domin wanzuwa a kan aiki(n kirki) ya fi aikata aikin wahala da tsanani… Don haka, sai mu haɗa da neman taimakon Allah ta’ala don samun taufiƙin cigaba da wanzuwa a kan wannan garwashin wuta na sanin sa da imani da shi tsarki ya tabbata gare shi…🤲🏽
✍️Ash-Shaikul Ārifu Billah

Al-Baqir Ibrahim Saminaka

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “BAYAN LAILATUL ƘADRI, SAI KUMA ME.?”