May 3, 2023
Bapalasdine Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Wuce Gona Da Iri Na HKI A Gaza

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Palasdinawa dake Gaza ta sanar da cewa da safiyar yau Laraba wani Bapalsdine daya ya yi shahada, yayin da wasu 5 su ka jikkata sanadiyar hare-haren sojojin HKI. Sanarwar ta ce shahidin shi ne Hashil Mubarak Salman dan shekaru 58.
Tun a jiya ne dai HKI ta rika kai wa yankin na Gaza hari, jim kadan bayan shahadar Khidr Adnan a gidan kurkukun ‘yan sahayoniya bayan da ya yi kwanaki fiye da 80 yana yajin cin abinci