March 6, 2023

Bankuna sun fara maido da tsaffin takardun kudi

 

Biyo bayan umarnin kotun koli kan ingancin tsaffin takardun Naira da kuma cigaba da karbar su har zuwa karshen wannan shekarar, wasu bankunan kasuwanci sun fara fito da tsaffin takardun kudaden suna ba wa jama’a.

 

Kamar yadda wata majiya ta bayyana, bankuna a jihohin Kano da birnin tarayya sun fara bada tsaffin kudin. Bankin Guarantee Trust da aka fi sani da GTBank ta bayyana cewa ta samu izini daga hukumomi daga sama kan umarnin cigaba da bayar da tsaffin takardun kudin.

Cikin makon nan ne dai gwamnan babban bakin Najeriya Godwin Emifele a yayin martanj ga umarnin kotu ta bayyana cewa sun riga da sun kone tsaffin takardun kudaden da suka karba daga hannun al’umma.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Bankuna sun fara maido da tsaffin takardun kudi”