January 7, 2023

bankin ya saka na daina amfani da tsohon kuɗin.

Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan ƙasar da su daina bayar da sabon kuɗi ga kwastomomin da suka shiga cikin banki domin karɓar kuɗi.

A maimakon haka babban bankin ya buƙaci bankunan da su saka sabbin kuɗin cikin na’urorinsu na cirar kuɗi na ATM.

Domin tabbatar da cewa kuɗin ya shiga hannun jama’a gabanin ranar wa’adin 31 ga watan da muke ciki da babban bankin ya saka na daina amfani da tsohon kuɗin.

Rahotonni sun ce babban bankin ya umarci bankunan da su gaggauta aiwatar da wannan umarni.

A watan Oktoban da ya gabata ne Babban Bankin Najeriya CBN, ya sanar da matakin sauya fasalin kuɗaɗen ƙasar, tare da umartar mutane da su mayar da tsofaffin kudaɗen banki don sauya musu da sababbi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “bankin ya saka na daina amfani da tsohon kuɗin.”