March 30, 2024

An kaddamar da bankin Musulunci na farko a kasar uganda

 

Ofishin shugaban kasar Ugandan ya bayyana cewa, an kaddamar da wani bangare na kungiyar Salaam Group mai hedkwata a kasar Djibouti a ranar Laraba a kasar Uganda a matsayin cibiyar hada-hadar kudi ta Musulunci ta farko a kasar.

Kaddamar da ayyukan bankin Salaam Bank Limited ya biyo bayan dokar da ta halasta aikin bankin Musulunci a kasar da ke gabashin Afirka a bara.

Kudi na Musulunci ya bi ka’idodin addinin Musulunci kamar hana biyan ruwa da kuma nisantar saka hannun jari a wasu ayyuka kamar caca.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ne ya jagoranci kaddamar da bankin a Kampala babban birnin kasar.

#Uganda

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “An kaddamar da bankin Musulunci na farko a kasar uganda”