October 11, 2021

Babban Labari: Nijeriya na daf da fara kera makamai

Daga Muhammad Bakir Muhammad


A yau Litinin ne shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya fitar da sanarwar cewa nan kusa kasar zata fara kera makamai don yakar matsalolin tsaro da ya dade yana addabar kasar.

Ya bayyana cewa ma’aikatar tsaro ta samu umarni daga gwamnatin tarayya don samar da ma’aikata da zata fara kera makamai saboda tunkarar ta’addanci da kuma dakile ta.

 

Shugaban ya bayyana hakan ne yau Litinin a yayin bude wani taro na kwana biyu da aka shirya don tattauna cigaba da aka samu kan ababe 9 da suka kasance kan gaba a wannan gwamnatin.

Shugaban ya nuna cewa samar da wannan ma’aikata zai rage yawan dogaron da kasar ke yi da wasu kasashe daban wurin samar da makaman yaki.

Ya kara da cewa aikin za’a kaddamar da shi ne karkashin kulawar wata bangare ta hukumar sojin Nijeriya dake da alhakin kula da samar da makamai (DICON).

A bayanin na shugaban kasa Buhari ya nuna cewa a bangare kokarin da suke na yaki da ta’addanci a kasar sun sayi rirajen yaki kiran “A-29 Super Tucano” guda 6.

Kasar dai ta Nijeriya ta kasance cikin matsalar tsaro, inda sojoji ke fafutukar yakar yan ta’adda a Arewa maso gabas, yan bindiga a Arewa maso yamma, rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta tsakiya, masu fafutuka ballewa da rajin kafa sabuwar ‘kasa a Kudu maso gabas da Kudu maso yamma, kana kuma ga matsalar masu garkuwa da mutane da ke addabar dukkan yankuna a fadin kasar.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Babban Labari: Nijeriya na daf da fara kera makamai”