Babban Bankin Najeriya Ya Ce Ba Zai Kara Wa’adin Sauya Kudi Ba
A yayin da ya rage kwanaki bakwai a kammalla sauya tsofaffin takardun kudi na Naira 1000, Naira 500 da Naira 200, manyan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki sun koka cewa har yanzu akwai karancin sabbin kudi a bankunan kasuwanci musamman a Abuja.
Wani bincike da Muryar Amurka ta gudanar na nuni da cewa, yawancin bankuna da ke Babban Birnin Tarayya Abuja suna sa sabbin kudade a na’urar su ta ATM amma kafin a ce kwabo sun kare, domin mutane suna layi tare da yin sammako domin cire kudi a na’urar.
Wani abu da ya dauki hankali kuma shine, ba a bada sabbin kudi akan kanta, amma ana karban tsoffin kudin.
A wasu jihohi na Arewa irin su Sokoto, Kan, Borno, Yobe da Katsina, labarin duka iri daya ne, a wasu lokuta ma ana samun mutane suna Jam’in sallah a cikin banki domin tsananin jira mai tsawon lokaci da suke yi saboda su canza kudaden su.
A bangaren Borno ta Kudu kuma, Sanata Mohammed Ali Ndume ne yayi korafi a madadin mutanen Jihar, inda ya ce yawancin al’umman Jihohin Arewa Maso gabas ba sa alaka da banki, kuma yanzu haka sun rufe shagunan su duka, domin suna tsoron karban tsofaffin kudi, gashi kuma babu sabbin a bankuna.
Masanin harkokin zamantakewan dan adam da gudanar da mulki kuma Malami a Jami’ar Abuja, Dokta Abdurrahman Abu Hamisu, ya yi tsokaci akan batun cewa, wannan tsari da gwamnati ta kawo na takura wa talaka ne, saboda haka yake kira akan a dauki darasi daga wasu kasashe da suke canjin kudin su babu matsala.
Abu yace kasashe irin su Saudi Arabiya da Ingila, ba sa bada wa’adi idan za su sauya kudi.
Shi kuwa masanin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati cewa ya yi, sauya kudin abu ne mai kyau amma shi ma ya yi suka akan wa’adin da aka sa na canjin kudi a bankuna da kuma yadda zai shafi talakawan kasa.
Majalisar Dokokin kasa ta kara sa baki, inda ta roki Babban Bankin ya kara wa’adin zuwa 30 ga watan Yuli na wannan shekara da muke ciki.
Abin jira a gani shi ne ko mahukunta za su saurari koken al’umma wajen biya masu bukatar kara wa’adin canji kudin.
©VOA Hausa.