September 10, 2021

Babandede yayi ritaya daga hukumar “NIS”

Daga Umar Ahmed

Shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya Muhammad Babandede, yayi ritaya bayan shafe shekaru 36 a bakin aiki.

Nadin jami’in a matsayin shugaban hukumar shige da ficen dai ya faru tun a watan Mayun shekarar 2016 a yayin da ya karba daga hannun tsohon shugaban ta Martin Kure Abeshi.

Hujjoji sun nuna sauye sauye da cigaba da dama wanda tsohon shugaban (Babandede) ya kawo a hukumar inda ya zamanantar da abubuwa da dama.

A yayin gudanar da wani taro, Babandede ya bayyana cewa ya bar hukumar “NIS” fiye da yadda ya sami ta.

Ya kara kuma da cewa ya samu damar cimma wadannan nasarorin ne daga hadin kai da ya samu daga abokan aikin sa.

Babandede ya alkawaranta cewa zai kasance jakada ga hukumar kana kuma yana shirye da mika hannun tallafi ga hukumar a duk lokacin da aka nemi hakan.

Yau yake barin hukumar bayan shafe shekaru 36 a cikin ta, kana kuma ya shafe shekaru 5 da watanni 4 a matsayin shugaban hukumar.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Babandede yayi ritaya daga hukumar “NIS””