January 16, 2024

BA ZAN JUYA BA MATUƘAR INA DA UBANGIJI

Marubuci: Al-Baqi Ibrahim Saminaka

Ɓangare na wata kyakkyawar tattaunawa da ta gudana tsakanin wani babban Malami da ɗabinsa da ke cikin ruɗani dangane da yadda watan Rajab zai amfane shi, ko yadda shi zai amfana da watan… Wata ƙila mu ma mu amfana daga tattaunawar. Ga ɓangaren yadda ta kaya;

Ɗalibi: Amm Malam… Da me WATAN RAJAB zai amfane ni alhalin ni dukkana zunubi ne?

Malami: Bawan Allah ai ahi watan Rajab ba na Arifai ne ba, domin su duk shekararsu ma Rajab ɗin ce. Watan Rajab na waɗanda suka nutse (A cikin zunubai) ne.

Ɗalibi: To ta yaya zan amfana daga wanan watan?

Malami: Zan ba ka wani mabuɗi zai amfane ka. Shin ka taɓa tambayar kanka mene ma’anar Hadisin nan da ke cewa: «Haƙiƙa Rajab wani kogi ne a cikin Aljanna»? Shin kana ga zai yiwu a rasa ziri/layi ko alamun wannan kogi a wannan duniyar?…

Malami: Dolen ka ka nemi wannan ziri/alama na watan Rajab a cikin rayuwarka… Wata ƙila ka same shi cikin yin Sukada a keɓance, ko istigfari cikin ƙasƙantar da kai, cikin zubar da hawaye, ko kuma a cikin yin wata salla, ko a cikin makokin Imamu Husaini (A), cikin nazarin wata aya, bayar da sadaƙa, ko kuma ma a cikin zaman karatu neman sani/ilimi. Dukkan waɗannan layuka/hanyoyi ne na wannan kogi na Rajab mai girma. Ka dudduba kada ka yanke ƙauna, domin mai jin ƙishi ba zaunawa yake yi ba, miƙewa yake yi ya nemi ruwan ƙila ma har ya kai ga ƙwaƙulan rami…

Ɗalibi: Allah ya taimake mu. Ɗan kara min.

Malami: RAJAB; Kogi ne na soyayya abin kwararowa, kogi ne na gafara, sutura, afuwa, ƴantuwa da ƴantarwa, karɓar tuba, kau-da-kai da kuma rangwame… Ka dogara ga Allah ka bar abinda ya riga ya wuce, ka ci moriyar abinda ya saura (Na lokacinka)…

Ɗalibi: Malam ka ba ni wani take (Slogan) nama, wanda koyaushe shi zai rinƙa ta da ni yana zaburar da ni.

Malami: Ɗauki wani take amintacce na gaskiya (ka riƙe shi da kyau), shi ne [BA ZAN JUYA BA MATUƘAR INA DA UBANGIJI]

SHARE:
Makala 0 Replies to “BA ZAN JUYA BA MATUƘAR INA DA UBANGIJI”