October 25, 2023

BA TA SAMU SUKUNI A BAYAN MAHAIFITA BA, HAR SAI DA TA BI SHI; AZ-ZAHARA (A).

Daga Malam Bakir Ibrahim Saminaka

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai, Tsira Da Aminci Su Ƙara Tabbata Ga Shugabar Mataye Faɗima, Da Babanta Da Mijinta Da Ƴaƴayenta Taurari Na Shiriya Kuma Jirage Na Tsira…

Shahadar Sayyidah Faɗima Az-Zahara (A). Abubuwan da suka faffaru da Sayyida Fadima (A) na bala’o’i, abubuwa ne masu girman gaske masu tsananin wahala. A bayan Wafatin Mahaifinta (S), yaya kwanakinta na ƙarshe suka kasance? Yaya girman masifun da suka riske ta?

Muna iya samowa daga zancen Babanta As-Sadiƙul Aminu (S), daga riwayar Ibn Abbas cewa; A wata rana Imamai Hasan da Husaini (A) su ka shigo wajen Manzon Allah (S), Al-Imam Ali da Sayyida Faɗima (A) ma su ka shigo, ɗaya bayan ɗaya, duk sanda ɗayansu ya shigo sai Manzon Allah (S) ya yi kuka. Har sabbai suka tambaye shi “Ya Ma’aikin Allah… Shin a duk cikin su babu wanda kake farin ciki da ganin sa ne?”

Subhanallah! Ahalul Kisa’in da ya lulluɓe a bargo ne fa, lallai rashin sani ya fi dare duhu.

Take kuwa ya yi azama dan kawar musu da wannan tunanin… Inda ya ce: “Haƙiƙa ni da su mu ne mafifita a cikin halittun Allah mai girma da buwaya, kuma babu wani da nake ƙauna fiye da su” A nan ya dinga lissafa falalolinsu ɗaya bayan ɗaya, tare da bayanin dalilin kukan nashi. Dangane da Faɗima (A) ya ce “Ita ce hasken idaniyata…” To mene ne ma’anar hakan? Ba abu ne da mu za mu iya riskar haƙiƙaninsa ba, girman daraja da ɗaukakar sha’anin Sayyida (A) da irin matsayinta a wajen Allah Ta’ala.

Haka nan Manzon Allah (S) ya ci gaba da cewa: “…Tamkar ina kallon ta ne; Wulaƙanci/tozarci ya shiga (ya kutsa) cikin gidanta, an kuma keta alfarmarta, an ƙwace mata haƙƙinta, an kuma hana ta gadonta, an karya mata haƙarƙarinta, an sanya ta yi ɓarin cikinta. Tana kiran Wayyo (Babana) Muhammda amma ba za a amsa mata ba, za kuma ta nemi taimako ba za a taimaka mata ba. Don haka ba za ta gushe ba a bayana tana abar cusa wa baƙin ciki, abar sanya wa damuwa, tana mai yin kuka!…”

 

ALLAH SARKI FAƊIMA !

Ita ce fa Az-Zahara ɗin nan, wacce alfarmarta na daga alfarma/hurumin Allah Maɗaukaki, haƙƙinta kuwa yana daga haƙƙoƙin Allah ne, wacce Allah da kansa fa yake yarda da yardarta, haka zalika yake yin fishi a yayin da ta yi fishi, ita ce wacce duk abinda aka yi mata na munanawa to ƙetare iyakar Allah Ta’ala ne. Ita ce fa amanar da mahaifinta Manzon Allah (S) ya tafi ya bari, amma ba ta sami hutu ba a bayan sa, har sai da ta bi shi cikin tsananin baƙin ciki, a tsakanin ƴan satikai. La Haula Wala Ƙuwwata Illa Billahil!

 

A ci gaban wancan Hadisin, sai Ma’aikin Allah (S) ya kara da cewa: “… Ita ce farkon wanda ya fara haɗuwa da ni daga cikin iyalaina, ta gabato min (Ta zo waje na abar sanya wa damuwa da baƙin ciki abar zalunta), saboda haka a yayin nan sai na ce: “Ya Allah ka la’anci wanda duk ya zalince ta, ka yi uƙuba ga wanda duk ya ƙwace mata haƙƙinta, ka taɓar da wanda ya taɓar da ita… Sai Mala’iku su amsa da cewa [Amin!]…”

{Al-Āmuliy Lis-Saduƙ: 112 zuwa 114}.

 

Mu ma nan haka muke amsawa da babbar [AMIN!], Haka duk muminai za su amsa da [Amin Ya Rabbal Alamin]… Allah Ta’ala ya girmama ladanmu na makokin Sayyida Faɗima (S) Allah ya gaggauta bayyanar Limamin zamaninmu (A.F).

INNA LILLAHI WA INNA LILLAHI RAJI’UN!

25/10/2023 = 09/04/1445

SHARE:
Makala 0 Replies to “BA TA SAMU SUKUNI A BAYAN MAHAIFITA BA, HAR SAI DA TA BI SHI; AZ-ZAHARA (A).”