February 13, 2023

AYATULLAH KHUMAINI Ayatullah Khumaini! Ayatullah Khumaini!!

 

Sunan daya mamaye duniya a karnin daya gabata daga 1970s Musamman nahiyar tarai sakamakon Juyin juya Halin Musulnci da yayi a Daula mai dunbin tarihi da karfi da Kuma iko.
Imam Khumaini
An haife Shi a garinsu da ake Kira Khumain a cikin Kasar Iran,24/09/1909
Ya taso karkashin kulawar Mahaifiyarsa da kanwar Mahaifinsa sakamakon Mutuwar Mahaifinsa ana gab da haihuwarsa, Kuma shine da na Karshe a wajan Mahaifinsa, sunan Mahaifinsa Sayyed Mustafa.
Ya Fara Karatun Addini a garinsu Khumain Inda ya haddace Kur’ani tun yanada Shekara 6,daga baya ya tafi Birnin ARAK dake Iran, bayan wani lokaci ya wuce zuwa Birnin Ilmi wato Qum Inda ya Dora karatunsa har ya Fara karantawa a hauzar Faidiyyah dake Qum.
Bayan Karatun Fiqhu da Usul da Adabul Araby (Adabin larabci) Sayyed Ruhullah ya Kara da Karatun falsafa da irfani a wajan Ayatullah Tabrizy da Mirza Ayatullah Sha’abady.
Yayi karatu Mai zurfi na Addini har yakai matakin Ijtihadi kuma ya fitar da RISALARSA wacce ta banbanta data saura Musamman a wasu Bubuka na Risalar Wace itace TAHRIRUL WASILA.
Yunkurin Imam gaban Sarkin Iran Shah
Sarkin Iran Shah Muhammad Ridha Bahlawy, sarki na Karshe a Daular bahlawiyyah, Wanda ya kasance Abokin Turawan Yamma Kuma Karan farautarsu ya Mika musu Iran da duk abinda suka mallaka nacigaba a Iran.
Turawa sun mamaye Iran sun shiga harkokin da Bai kamata ba su shiga, an watsar da tsarin mulkin kasa (constitution). Sarki Muhd Ridha Shah ya watsar da bukatun Talakawa ya maida hankalinsa akan bukatun Turawa Musamman America har takai ga an Sanya dokar Hana hukunta Turawa idan sukayi laifi a cikin Kasar ta iran.
al’ummah sun yunkura sosai wajan Kira ga Gwamnatin Shah da su dawo Kan tsari na Asali Amma aka watsar da bukatun su.
An Kashe da yawa da masu jagorantar kin jinin Zaluncin da yunkurin sauya tsarin mulkin kasa wasu Kuma an rufe su a kurkuku.
Ayatullah Sayyed Ruhullah Khumaini ya fara kiransa ga Sarki Shah ta hanyar Wasiku daga Qum Musamman daga Makarantar Faidiyyah Wanda hakan yasa ya Fara fuskantar matsi daga Malaman Addini saboda Hauza Bata shiga Harkokin Siyasa Amma Imam ya dake akan hakan har takai ga fara jawabansa na Siyasa da Kiran Sarki Shah ya dawo kan tsari Kuma ya saurari koken Talakawa da mabukata, Maganganun Imam sun Fara tasiri sosai wajan Sanya mutane suna fitowa har tai ga Sarki Shah ya Kama Imam Khumaini a Sanya a Kurkuku Wanda hakan shine dalilin fitowar Jama’a a Biranan Iran suna zanga-zanga, Hauzar Qum Kuma ta fitar da Sakon cewa Imam Khumaini Marja’i ne( Wanda a tsarin Iran haramun ne hukunta Maraji’ai) Dole tasa aka sake Shi bayan kwanaki kadan.
Bayan fitowar imam bai dakata ba haka yaci gaba da Kiran Jama’a su fito Domin dawo da Tsarin da aka bunne.

HIJIRA
Bayan Sarki Shah ya kasa tsayar da Kiran Imam Khumaini sai suka yanke Hukuncin fitar da Imam daga Iran da raba Shi da Dalibansa da sauran Jama’a a Iran har tsawon Shekara goma sha biyar 15, Amma bai caza komai ba.
Turkiya (Turkey)
04/11/1964 Aka dauki Imam aka fitar dashi zuwa Ankara (Babban Birnin Turkiya), daga nan Kuma zuwa Bursa (daya daga Biranan Turkiya) Har zuwa September 1965.
IRAKI (IRAQ)
A Ranar 4 ga September 1965, Aka fitar dashi zuwa Baghdad-Iraq Inda daga nan ya wuce zuwa Karbala, daga Karbala ya tafi Birnin Najaf Inda ya Zauna Acan kusan Shekara Goma Sha Uku 1978, zamanin Saddam Hussain.

Paris
Ranar 6 ga October 1978, Imam Ya sanar da fitarsa daga Iraqi ya shiga Kuwait Amma suka ki karbarsa Inda daga anan ya tafi Neauphle-le-Château Paris, Inda ya Sami damar tattaunawa da Yan jarida sosai wajan isar da sakonsa zuwa ga cikin Iran da sauri Wanda yai Kiran Jama’a dasu fito Domin kawar da Gwamnatin Shah.

Al’ummar Iran sun amsa kiransa Inda suka fito Kauyuka da birane da tituna tun Yan sanda da sojoji suna kokarin tsaida mutane har suka kasa, wanda ya jawo fitar Gaggawa da Sarki Shah yayi daga Iran fitar dabai Kara dawowa ba har zuwa yau .
Ranar 1 ga watan February 1979, Imam Khumaini ya Sauka a Iran bayan fitarsa na tsawon Shekara goma sha biyar 15 da yayi, Wanda bayan isarsa da kwanaki aka Sami Nasarar Kifar da Gwamnatin Shah ta Daular Bahlawiyyah Daular Farisa, Daula mai Babban Tarihi, Wace aka Canzata da Gwamnatin Musulnci daga Nan Iran Yau Shekara 41 kenan Take JUMHURIYYAR MUSULNCI TA IRAN Wacce AYATULLAHIL UZMA IMAM ASSAYYED RUHULLAH MUSTAFA ALMUSAWY ALKHUMAINI (Qs) ya Assasa.

Ya Rasu a Shekara ta 1989, bayan Rashin Lafiya daga nan aka Sanya daya daga Manyan Dalibansa wato Ayatullah Sayyed Ali Khamina’i a matsayin Sabon Jaroran Juyin juya Halin Musulnci a Iran.

Yayansa
Sayyed Mustafa
Sayyed Ahmad
Sayyeda Siddika
Sayyeda Faridha
Sayyeda Zahra.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “AYATULLAH KHUMAINI Ayatullah Khumaini! Ayatullah Khumaini!!”