May 19, 2024

Jagora ya yi addu’ar Allah ya dawo da shugaba Raeisi lafiya bayan wani hatsarin jirgin sama

Jaridar ahlulbaiti ta nakalto daga tashan press tv  ta kasar Iran cewar

A yau Lahadi, 19 ga Mayu, 2024 misalin karfe 5:57 na yamma Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana damuwarsa bayan da jirgin helikwafta da ke dauke da shugaban kasar Ibrahim Raeisi ya yi a wani yanki mai tsaunuka da ke arewa maso yammacin kasar Iran.

Ayatullah Khamenei ya ce “Muna fatan Allah Madaukakin Sarki ya mayar da shugaban kasa da ake girmamawa da kuma abokan aikinda  zuwa ga al’ummarsa

Jagoran ya bukaci dukkan al’ummar Iran da su yi addu’a don lafiya da amincin shugaba Raeisi da sauran ma’aikatan gwamnati da ke cikin jirgin

Jirgin mai saukar ungulu yana jigilar Shugaba Raisi, Ministan Harkokin Waje Hossein Amir-Abdollahian da wasu jami’ai da dama lokacin da ya fuskanci matsala

Lamarin ya faru ne a dajin Dizmar da ke tsakanin garuruwan Varzaqan da Jolfa. Shugaba Raeisi yana dawowa ne daga wani aiki na ƙaddamar da madatsar ruwa a kogin Aras tare da shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev.

Ana ci gaba da gudanar da wani gagarumin aikin bincike akan lamarin.

@ Fassarar Hauwa Mohammed suleman.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Jagora ya yi addu’ar Allah ya dawo da shugaba Raeisi lafiya bayan wani hatsarin jirgin sama”