May 21, 2024

Asalin yadda hankaka yake yin karuwa

Asalin yadda hankaka yake yin karuwa shine, kamar kowanne tsuntsu shima hankaka macen tana yin kwai ne kamar guda uku zuwa shida. Sannan kuma sai tayi kwanci daganan ta kyankyashe. Bahaushe yace “hankaka maida dan wani naka”, wannan karin maganar wani hasashe ne na malam bahaushe dan yana ganin hankaka kandauki kwai na kaza ko na agwagwa ko gunya ya tashi yayi sama dashi. To me yake dashi?
shidai wannan kwan hankaka yana kaishi ne can kan shekar shi inda macen ke kwanci, daidai lokacin da zata kyankyashe ne kuma wannan kwan da namijin hankaka ya dauko shima kuma ya rube, shine zai zama abincin yan tsakin hankakin.

©  Salahdin Mansur Bauchi

SHARE:
Halittun gida Dana daji 0 Replies to “Asalin yadda hankaka yake yin karuwa”