November 22, 2022

Arewacin Najeriya zai rika samar da gangar mai dubu 120 a kullum

Gwamnatin Najeriya ta ce kashi na farko na aikin samar da man fetur da kuma iskar gas daga yankin arewacin kasar zai taimaka mata samar da gangar mai  dubu 120 kowacce rana da kuma kubik miliyan 500 na iskar gas kowacce rana a yankin, abin da zai kai ga samar da hasken wutar lantarki mai karfin megawatt 300 da kuma kamfanin samar da takin zamanin da zai rika samar da tan dubu 2 da 500 kowacce rana.

Wannan ya biyo bayan kaddamar da aikin man wanda za a rika fitar da shi zuwa kasuwannin duniya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi yau a Jihar Bauchi, sakamakon kwangilar da kamfanin man NNPC ya kulla da kamfanin NNDC da kuma AOML.

Shugaban kasa Buhari ya sanya shirin hako man daga yankin arewacin Najeriya a cikin manyan ayyukan da gwamnatinsa za ta mayar da hankali akai, duk da sukar da ke zuwa daga bangarori da dama wadanda ke cewar asarar kudaden gwamnati ake yi domin babu yawan mai da gas da Najeriya za ta ci moriyarsa a yankin.

Sakamakon aikin da aka yi a iyakokin Bauchi da Gombe, kamfanin man NNPC ya ce yawan man da Najeriya za ta samu daga yankin zai kai ganga biliyan 19, yayin da yawan iskar gas kuwa zai kai kubik biliyan 500, makamashin da yau ya zama tiraren dan goma saboda yadda ake bukatarsa a kowanne sako na duniya.

Ana sa ran wannan aiki ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihohin da abin ya shafa da arewacin kasar da kuma Najeriya baki daya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Arewacin Najeriya zai rika samar da gangar mai dubu 120 a kullum”