March 16, 2024

Hare-hare ta yanar gizo sama da 90,000 da suka samo asali daga Ukraine da Arewacin Amurka sun auka a tashoshin zabe.

Jaridar ahlulbaiti ta nakalto Kuma ta fassara daga tashar yada labarai ta Al-mayadeen bangaren larabci cewar,

Shugaban Kamfanin Solar Group, reshen Rostelecom, Igor Lyapunov, ya bayyana jiya Asabar cewa, a ranar farko ta zaben kasar Rasha, sama da hare-hare ta yanar gizo sama da 90,000 da suka samo asali daga Ukraine da Arewacin Amurka sun auka a tashoshin zabe.Ummmm

Lyapunov ya bayyana cewa irin wadannan hare-haren na intanet da ba a taba ganin irinsa ba na nuni da cewa kasashen yammacin duniya na yaki da Rasha, inda ya kara da cewa hare-haren sun samo asali ne daga “Ukraine da sauran wurare a yammacin Turai da kuma Arewacin Amirka.”

Ya kara da cewa, an kai wani babban hari ta yanar gizo da ba a taba yin irinsa ba jiya da karfe 12:47 agogon Moscow, inda aka nufi dandalin zabe na lantarki da ya kai sama da matsi miliyan 2.5 a cikin dakika daya, nauyin da ya jawo tsaiko a tashar.

Da sanyin safiyar yau, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Washington na amfani da masu satar bayanai tare da tattara bayanan batanci da za’a buga a jajibirin zabe da kuma ranar zabe domin yin tasiri a kan yadda ake kada kuri’a a zaben shugaban kasar Rasha.

 

© Al-mayadeen

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Hare-hare ta yanar gizo sama da 90,000 da suka samo asali daga Ukraine da Arewacin Amurka sun auka a tashoshin zabe.”