January 8, 2023

Anyiwa sojojin Côte d’Ivoire 49 da aka kama a watan Yulin shekarar 2022 afuwa jiya Jumma’a

Mai magana da yawun gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali, ya bayyana a yau Asabar cewa, shugabannin gwamnatin rikon kwaryar kasar, sun yiwa daukacin sojojin Côte d’Ivoire 49 da aka kama a watan Yulin shekarar 2022 afuwa jiya Jumma’a.
A ranar 10 ga Yulin shekarar 2022 ne, aka kama sojojin Côte d’Ivoire 49, bayan da suka isa filin jirgin saman Bamako, babban birnin kasar. Gwamnatin rikon kwarya ta Mali, ta bayyana su a matsayin sojojin haya, kuma ta bukaci a gurfanar da su a gaban kotu. Kasar Côte d’Ivoire dai ta bukaci Mali da ta gaggauta sakin sojojinta, tana mai cewa wadannan sojojin sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta daban-daban da tawagar MDD dake Mali (MINUSMA) a watan Yulin shekarar 2019, don samar da tsaro da taimakon kayan aiki ga kasar.

© Cri (Ibrahim)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Anyiwa sojojin Côte d’Ivoire 49 da aka kama a watan Yulin shekarar 2022 afuwa jiya Jumma’a”