Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

October 22, 2021

Annabi Muhammad (s.a.w.a)…Manzon Rahama Da Kyawawan Halaye

Malam Muhammad Awwal Bauchi


Kamar yadda a makon da ya gabata muka yi alkawarin fara bude wannan fili na “Rayuwar Magabata” da dubi cikin tarihi da rayuwar Manzon Allah, Muhammad (s.a.w.a) don daukar darussan da suke ciki.

Girman matsayin da Annabinmu Muhammadu (s.a.w.a) yake da shi ya kasance wani yanayi maras tamka cikin tarihin bil’adama. Wannan girman matsayi kuwa ya samo asali ne sakamakon wasu dalilai masu yawa sai dai ana iya takaita su cikin wasu tushe ko mabubbuga guda hudu:

Mabubbuga Ta Farko: Zabi Na Ubangiji:

Siffa ta farko da Annabi (s.a.w.a) ya kebanta da ita wacce kuma ta ba shi irin wannan girman matsayi da yake da shi, ita ce cewa Allah Madaukakin Sarki shi ne Ya zabe shi da kuma kusato da shi kusa da Shi sama da dukkanin bil’adama, kai sama da dukkanin halittu ma; don kuwa Shi Ubangiji shi ne yake da wannan siffa kamar yake fadi cikin Suratul Kasas 28: 68: “Kuma Ubangijinka Yana halitta abin da Yake so kuma Yake zabi”. Allah Madaukakin Sarki, bisa mashi’arsa, Ya so ya samar da wasu ababen koyi, masu wasu siffofi na kyawu da kamala, a cikin bil’adama, don su zamanto musu abin koyi a rayuwarsu. Wadannan kuwa su ne Annabawa da Manzanni, wadanda su ne kolin kamala cikin bil’adama. Suna da duk wata siffa ta alheri da kamala, duk da cewa daukaka da falalar da suke da ita ta bambanta a tsakaninsu, kamar yadda Allah Yake fadin cewa: “Wadancan Manzannin mun fifita sashensu a kan sashe”. Cikin ikonsa kuwa sai ya sanya Annabinmu Muhammadu (s.a.w.a) shi ne mafifici da daukaka cikin dukkanin wadannan Annabawa da Manzannin.

 

Haka Allah Madaukakin Sarki Ya so Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance mafificin daraja da matsayi hatta a tsakanin Annabawa da Manzannin ballantana sauran bil’adama kuma. Shi ya sa ma kamar yadda ya zo cikin littafin Bihar al-Anwar, Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Ni ne shugaban dukkanin ‘ya’yan Adamu. Ba bisa alfahari ba, ni ne kuma Cikamakin Annabawa kuma shugaban masu tsoron Allah, kana kuma Manzon Ubangijin talikai”. Daga wannan bayanin za mu iya fahimtar wannan hakika ta cewa shi ne mafificin daraja kana kuma mafi soyuwan halitta a wajen Allah Madaukakin Sarki, don kuwa kamar yadda ya zo cikin Suratul Hujurat 49:13: Lalle mafificinku daraja a wurin Allah, shi ne mafificinku a takawa (tsoron Allah)”, shin akwai wani mutum a fadin duniyar nan da za a iya kwatanta tsoron Allahnsa da na Annabi (s.a.w.a)? Babu. Ko shakka babu, shi ne mafi girman tsoron Allah cikin mutane, don haka shi ne mafi daukaka a wajen Allah.

 

Wannan zabi da Allah Yayi masa da kuma fifita shi bisa sauran bil’adama yana tattare da wasu abubuwa a wannan duniya da kuma lahira. Daga cikinsu kuwa har da abubuwan da riwayoyi suka zo da su da suke nuni da girman matsayin da yake da shi da suka hada da batun cewa shi ne mutumin farko da kasa za ta fara tsagewa don ya fito a ranar Kiyama lokacin da ake tayar da mutane. Da kuma cewa shi ne Annabin farko da zai fara neman ceto ga al’ummarsa a wajen Allah. Don kuwa al’ummomin sauran Annabawa za su tafi wajensu da bukatar su nema musu ceto a wajen Allah, to amma babu guda daga cikinsu da zai iya neman wannan ceton gabannin Annabi (s.a.w.a); haka nan kuma shi ne mutumin farko da za a bude masa Aljanna, sannan kuma shi ne mutumin farko da zai shiga Aljanna, kamar yadda aka ruwaito shi yana cewa: “Ni ne mutumin farko da zan kwankwasa kofar Aljanna, sai Mai gadinta ya ce: Kai ne wa? Sai in ce: Ni ne Muhammadu. Sai ya ce: Bari in tashi in bude maka, ban taba tashi don bude wa wani kafinka ba, sannan kuma ba zan tashi don bude wa wani a bayanka ba”. Shin akwai wani girman matsayin da ya wuce wannan?

 

Mabubbuga Ta Biyu: Girman Sakon Da Aka Aiko Shi Da Shi

A biyo mu  rubutu na gaba…

SHARE:
Raruwar Magabata 2 Replies to “Annabi Muhammad (s.a.w.a)…Manzon Rahama Da Kyawawan Halaye”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

2 thoughts on “Annabi Muhammad (s.a.w.a)…Manzon Rahama Da Kyawawan Halaye

  Author’s gravatar

  muna muku godiya da farin ciki bisa kokarinku .

  filin Rayuwar iyali muna jin dadinsa
  sosai amma bakwa kawoshi sosai muna gaida sheikh Basir bisa kokarinsa akan wannan fili afadawa shehi cewar muna gaidashi sosai muna gaida dukkan jamaarku Allah yaja kwana ya taimaki jaridarmu ta ahlulbaiti

  Author’s gravatar

  ALHAMDULILLAH MUNGODE WA ALLAH YA DAWOWAR WANNAN JARIDAR ALLAH YASA MUDACE.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *