October 28, 2021

Annabi Muhammad (s.a.w.a)…Manzon Rahama Da Kyawawan Halaye

Cigaba daga rubutun da ya gabata…

Mabubbuga Ta Hudu: Nasarar Da Ya Samu

Hakika Manzon Allah (s.a.w.a), cikin dan karamin lokaci na rayuwarsa ya samu nasarar aiwatar da wasu manyan ayyukan da ake ganinsu a matsayin mafi girman nasara cikin tarihi. Irin wadannan ayyuka nasa kuwa sun ba wa mafiya yawa daga cikin masana da malaman tarihi hatta wadanda ba musulmi ba mamaki. A saboda haka ne ma babban masanin tarihin nan Ba’amurke Micheal H. Hart, cikin littafinsa: ‘The 100: A Ranking of the Most Influential Person in History wanda ya kumshi jerin sunayen mutane 100 da suka yi tasiri cikin tarihin bil’adama ya sanya Annabi (s.a.w.a) a matsayin mutumin farko cikin jerin wadannan sunayen. Mene ne dalilinsa na hakan, ga abin da ya ke cewa: “Zaben da na yi wa Muhammadu a matsayin mutum na farko a jerin sunayen manyan mutanen duniya zai ba wa wasu masu karatu mamaki, wasu kuma za su yi inkari; amma shi ne wani mutum makadaici a tarihi, wanda ya sami madaukakiyar nasara a dukkan bangarorin da suka shafi addini da ma wadanda ba su shafe shi (duniya) ba”. Marubucin ya ci gaba da cewa: Hakika Muhammadu ya samu nasarar kafawa da kuma yada daya daga cikin mafiya girman addinai a duniya, sannan ya zamanto daga cikin mafiya ficen manyan ‘yan siyasa. A irin wadannan ranaku sannan kuma bayan gushewar kimanin karnoni 13 da rasuwarsa, amma har ya zuwa yanzu yana da gagarumin tasiri”.

Wadannan su ne mabubbugar daukaka cikin tarihin Manzon Allah (s.a.w.a).

A hakikanin gaskiya a wannan zamanin da muke ciki da ake da hanyoyin sadarwa kala-kala sannan kuma ga irin gurguwar fahimta da wasu, shin makiya ne ko kuma wasu masoyan ma, suka yi wa tarihin rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a), akwai bukatar sake dubi cikin tarihin rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a) da mahanga ta zamani wacce hakan za ta kara fito mana da girman matsayin da yake da shi, da kuma magance mana wasu shubuhohi da wasu suke shigowa da su cikin wannan addini ta yadda ake ganinsa da wani irin kallo na daban.

Abu na biyu mai muhimmanci shi ne cewa sake dubi cikin rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a) zai taimaka mana wajen tarbiyyartar da ‘ya’ya da kuma zuriyarmu. Don kuwa tarihin rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a) cike yake da irin wadannan kissoshi da za su iya zama darasi ga rayuwar. A bangare guda kuma da isar da wannan sako zuwa ga sauran al’ummomin duniya, wadanda makiya suka cika kunnuwansu da wasu labarai marasa tushe dangane da shi kansa Manzo din da kuma sakon da ya zo da shi.

Da yardar Allah a fitowa ta gaba za mu yi kokarin bayani dangane da yadda rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a) ta kiyaye da kuma tabbatar da karama da kuma mutumcin dan’adam wanda shi ne mafi girma da daukakar komai a gare shi sabanin ikirari na karya da wasu suke yi kan batun kiyaye hakkoki da kuma karamar dan’adam.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Annabi Muhammad (s.a.w.a)…Manzon Rahama Da Kyawawan Halaye”