October 23, 2021

Annabi Muhammad (s.a.w.a)…Manzon Rahama Da Kyawawan Halaye

Cigaba daga rubutun da ya gabata…

Mabubbuga Ta Biyu: Girman Sakon Da Aka Aiko Shi Da Shi

Haka nan Allah Madaukakin Sarki Ya sanya sakon da Ya aiko Annabinmu (s.a.w.a) da shi, ya zamanto mafi cika da kamalar sakonsa zuwa ga bil’adama. A fili yake cewa Annabawan da suka gabata sun zo wa al’ummominsu da sakonni daga wajen Allah, to amma Allah Madaukakin Sarki Ya sanya sakon Musulunci ya zamanto shi ne mafi daukaka da kuma cikan dukkanin sakonnin da Ya aiko zuwa ga bil’adama. Saboda kuwa wani sako ne da ya tabo dukkanin bangarori na rayuwar dan’adam. Sako ne da ya damu da bangaren ruhi, kamar yadda ya damu da bangaren jikin dan’adam. Ya damu da duniya, a daidai lokacin da kuma bai yi watsi da lahira ba. Ya ba wa hankali muhimmanci, ba tare da kuma ya rufe ido ga bangaren tausayi ba. Don haka sako ne da ke da kamala da daidaito. Sako ne mai gyarawa da kuma shiryar da dan’adam a dukkan zamunna da kuma dukkanin bigirori, matukar dai aka fahimce shi hakikanin fahimta.

Mabubbuga Ta Uku: Kyawawan Halaye Da Dabi’u

Manzon Allah (s.a.w.a) ya kebanta da mafi kyawu da daukakar halaye, duk kuwa da irin wannan al’umma ta jahiliyya da ya tashi a cikinta. Mai yiyuwa ne za a iya fahimtar girman matsayin da wadannan halaye na Manzon Allah (s.a.w.a) ne idan aka yi la’akari da cewa sun bayyana ne a cikin wata al’umma wacce ta ke rayuwa cikin mafi kolin koma baya. Amma haka Annabi (s.a.w.a) ya rayu cikinsu da irin wadannan kyawawan halaye da dabi’u nasa ta yadda hatta makiyansa sun shaide shi da irin wadannan kyawawan halaye, don haka ne Allah Madaukakin Sarki Ya siffanta shi da cewa: “Lalle hakika kana a kan halayen kirki masu girma”.

Ko shakka babu Annabi (s.a.w.a) ya nuna wani irin hali da dabi’a maras tamka cikin wannan al’umma ta jahiliyya wacce ta ci baya. Saboda kuwa a fili yake cewa a lokacin da mutum yake rayuwa cikin wata al’umma ma’abociya ci gaba da kuma kyawawan halaye na gaba daya, ko shakka babu irin wadannan halaye da dabi’u za su yi tasiri cikin rayuwarsa, komai kashin tasirin kuwa. Haka nan idan aka sami akasin hakan. Tarihi ya shaida cewa al’ummar da Annabi ya taso a cikinta wata al’umma ce ta jahiliyya da dukkanin ma’anar kalmar. Al’umma ce wacce ta yi kaurin suna wajen rashin tausayi hatta a tsakaninsu, ina ga kuma wani na waje. Don haka ne ma ake ganin yadda rayuwarsu ta ke cike da yakukuwa da zubar da jini. A takaice dai ba a wuce gona da iri ba idan aka ce suna rayuwa ce irin ta dabbobi, mai karfi ya murkushe mara shi. To amma sai ga shi Manzon Allah (s.a.w.a) ya tashi a cikinsu amma da irin wadannan kyawawan halaye maras tamka duk kuwa da kiyayya da cutarwar da suke masa. An ruwaito cewa a lokacin da Annabi (s.a.w.a) zai tafi Da’ifa don isar da sakon Musulunci, mutanen Da’ifan sun cutar da shi cutarwa, da suka hada da zagi, cin mutumci, da kiransa da dukkanin sunaye na batanci irin su makaryaci, mai sihiri, mahaukaci, suna jifarsa da duwatsu har sai da suka farfasa masa jiki. Amma a irin wannan yanayi da yake ciki, a lokacin da Mala’ikun Allah suka zo suka ce masa: “Ya Muhammad, kai ne mafi daukakar halittun Allah, umurninka abin aikatawa. Gaya mana abin da kake so mu aikata da wadanda suka cutar da kai”. Riwayoyi sun ce ba Mala’ika guda ba ne ya zo, Mala’iku daban-daban ne suka zo da suka hada da masu kula da iska da ruwa da sauran abubuwa masu karfin gaske da suke tafiyar da duniya. Suna jiran umurninsa ne kawai. Amma duk da irin wannan yanayi da yake ciki, da irin wannan cutarwar da mushirikai suka yi masa, amma maimakon yayi musu addu’ar a halakar da su, sai ya daga kansa sama ya ce: “Ya Allah, Ka shiryi wannan al’umma tawa, saboda su din ba su sani ba ne”.

Assalamu alaika Ya Rasulallah! Wannan wani irin halitta ce? Shin akwai wani kyakkyawan halin da ya wuce wannan?

Irin wadannan kyawawan halaye na Ma’aiki (s.a.w.a) sun kara fitowa fili ne yayin mu’amalarsa da mafiya girman makiyansa wadanda suka shafe rayuwarsu wajen yakansa da kuma kashe masa wasu daga cikin mafiya soyuwa cikin sahabbansa. Duk da irin wannan kiyayya da cutar da shi da suka yi, amma a lokacin da ya samu nasara a kansu, wato ranar Fathu Makka, sai ya ce musu: “Ku tafi ku din nan ‘yantattu ne”. Kai abin ma bai tsaya nan ba, lokacin da Abu Sufyan ya zo wajensa ya ce masa: Ya Manzon Allah, ka yi afuwa wa dukkanin mutane kuma ni ma ina daga cikinsu, to amma da yake ni ina da matsayi a cikin al’umma ta, ina bukatar wata alfarma ta daban daga wajenka. Sai ga Manzo (s.a.w.a) ya rufe ido kan dukkanin kiyayya da Abu Sufyan ya nuna masa, inda ya ce: “Ku sani duk wanda ya shiga gidan Abu Sufyan ma ya tsira”. Haka ya aikata da Abdullah bn Ubaiy, shugaban munafukan Madina, wanda ya aikata abin da ya aikata wa Annabi (s.a.w.a), to amma a lokacin da ya zo mutuwa ya bukaci Annabi (s.a.w.a) da ya ba shi rigarsa don a yi masa likkafani da ita, haka Annabi ya amsa masa wannan bukata tasa.

Wannan wani bangare ne na irin wadannan kyawawan halaye na Ma’aiki (s.a.w.a) wadanda ya sami nasarar sauya tarihi da su.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Annabi Muhammad (s.a.w.a)…Manzon Rahama Da Kyawawan Halaye”