April 24, 2023

Anakwashe ‘yan kasashen waje yayin da wasu gungun ‘yan tawaye suka yi artabu a birnin Khartoum na kasar Sudan

 

Kasashen sun yi ta tururuwa domin kwashe jami’an diflomasiyyarsu da ‘yan kasar daga babban birnin Sudan a ranakun Asabar da Lahadi.

Kasashen ketare na yin gaggawar fitar da ‘yan kasarsu daga Sudan a daidai lokacin da bangarorin soji da ke gaba da juna ke fafatawa a babban birnin kasar Khartoum inda miliyoyin mazauna kasar suka makale a cikin gidajensu, inda yawancinsu ke fama da karancin ruwa da abinci.

Rikicin da ya barke a ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin sojojin kasar da kungiyar ‘yan ta’addar Rapid Support Forces (RSF) ya haifar da matsalar jin kai, inda aka kashe mutane akalla 420 tare da barnata tankokin yaki da kona gidaje da shaguna da aka yi awon gaba da su tare da kona su

Yayin da jama’a ke yunkurin tserewa hargitsin a karshen mako, gwamnatocin kasashen waje sun fara saukar jiragen sama tare da shirya ayarin motocinsu a birnin Khartoum domin fitar da ‘yan kasarsu.

Amurka ta ce dakaru na musamman da ke amfani da jirage masu saukar ungulu kirar MH-47 Chinook, sun kutsa cikin babban birnin kasar Sudan da ke fama da yaki daga wani sansani na Amurka da ke Djibouti, inda suka kwashe sa’a guda a kasa wajen fitar da mutane kasa da 100.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Anakwashe ‘yan kasashen waje yayin da wasu gungun ‘yan tawaye suka yi artabu a birnin Khartoum na kasar Sudan”