June 7, 2024

Ana murkushe daliban da ke zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a Amurka

Jaridar ahlulbaiti ta ruwaito daga tashar Al-Mayaden ta larabci cewar.

Ana ci gaba da murkushe daliban da ke zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a jami’o’i, ba wai ‘yan sanda da jami’an gudanarwa kawai ba har ma da masu daukar ma’aikata.

Wani kamfanin lauyoyi na kasa da kasa Winston & Strawn, ya janye tayin aikin da ya yi wa wata dalibar da ta kammala digiri a fannin shari’a a Jami’ar New York, Ryna Workman, saboda ta rubuta wata sanarwa mai goyon bayan Falasdinu a cikin imel a matsayin wani bangare na matsayinta na shugabar kungiyar lauyoyin dalibai, inda ta bayyana cewa. “Isra’ila ce ke da alhakin wannan babban asarar rayuka.”

Wani kamfanin lauyoyi Davis Polk & Wardwell ya bayyana cewa zai soke tayin uku ga dalibai a Harvard da Columbia saboda ra’ayinsu na goyon bayan Falasdinu.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin korar wasu ‘yan kasashen Turai tara daga kasar Girka saboda halartar zanga-zangar neman goyon bayan Falasdinu a harabar makarantar koyon shari’a ta jami’ar Athens a watan da ya gabata.

© Fassarar:Aisha Abubakar

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ana murkushe daliban da ke zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a Amurka”