November 23, 2023

Ana Gab Da Samun Matsaya Kan Batun Dakatar Da Bude Wuta A Gaza

 

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyah ya sanar da cewa, kungiyar tana gab da cimma matsaya kan batun tsagaita wuta a Gaza, a yakin da Isra’ila take kaddamarwa kan al’ummar yankin tun daga ranar 7 ga watan Oktoba da ya gabata.

Haniyah ya ce a cikin wani takaitaccen sako da kungiyar Hamas ta fitara yau Talata a kan manhajar Telegram, “Kungiyar ta mika amsa ga Qatar da masu shiga tsakani, kuma muna gab da cimma yarjejeniya ta dakatar da bude wuta.”

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar ta zargi Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kaucewa duk wasu hanyoyi na cimma yarjejeniyar “musayar fursunoni” da kuma jan kafa wajen kammala ta.

Tashar talabijin ta Palestine Today ta bayar da rahoton cewa, “Kungiyoyin Jihad Islami da Hamas sun amince bisa ka’ida kan sharuddan yarjejeniyar fursunoni, tare da nuna cewa ya hada da “tsagaita wuta na kwanaki biyar” da shigar da manyan motoci 300 na kayan gaji zuwa Gaza, gami da magunguna da man fetur, da kuma sakin fursunoni 50, da suka hada da yahudawa ‘yan share wuri zauna da kuma wadanda suke dauke da fasfo na wasu kasashe da suke tsare a Gaza, yayin Isra’ila kuma za ta saki fursunonin Falastinawa 300 da suka hada da mata da kananan yara da take tsare da su.

Mai magana da yawun bangaren tsaron kasa a fadar White House, John Kirby, ya sanar da cewa masu shiga tsakani kan yarjejeniyar sun kusa cimma matsaya.

 

 

©V.O.H

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ana Gab Da Samun Matsaya Kan Batun Dakatar Da Bude Wuta A Gaza”