December 7, 2022

Ana cigaba da gasar cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a kasar Qatar.

Jiya Talata ne, aka ci gaba da wasan neman shiga zagayen kasashe 8 da za su fafata a gasar cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a kasar Qatar. Kasar Morocco ta doke Spaniya wadda ake sa ran za ta lashe kofin gasar, inda aka kammala wasan ta zama ci 3 da 0 bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida. A daya wasan kuma kasar Portugal ta doke Switzerland da ci 6:1, inda ‘dan wasan Portugal Goncalo Ramos ya jefa kwallaye uku rus.
Yanzu Portugal da Morocco za su fafata a wasan kusa da na karshe.

Cri(Jamila)

SHARE:
Labarin Wasanni 0 Replies to “Ana cigaba da gasar cin kofin kwallon kafan duniya dake gudana a kasar Qatar.”