May 7, 2023

​Ana Ci Gaba Da Yaki A Kasar Sudan A Yayinda Wakilan Sojojin Kasar Ke Tattaunawa A Saudia

 

A dai dai lokacinda wakilan sojojin da suke fafatawa da juna suke fara tattaunawa don dawo da zaman lafiya a kasar Sudan, an ci gaba da yaki a safiyar yau Lahadi a sassa da dama a cikin birnin Karthun babban birnin kasar.

Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai daga kasar Sudan suna cewa an ji karar tashin bindigogi da kuma tashin boma bomai a birnin Karthum.

Sojojin kasar sun bada labarin kashe sojojin RSF da dama, sun kuma lalata motocinsu da dama sun kuma kama wasu a hannu.

A halin yanzu dai an shiga mako na ukku kenan da fara yaki a kasar ta Sudan sannan ya zuwa yanzu mutane fiye da 500 sun rasa rayukansu a yayinda wasu dubban suka ji rauni.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Ana Ci Gaba Da Yaki A Kasar Sudan A Yayinda Wakilan Sojojin Kasar Ke Tattaunawa A Saudia”