April 13, 2023

Ana Ci Gaba Da Shirye-Shiryen Raya Ranar Quds Ta Duniya A Kasashe Da Dama

Ana ci gaba da gudanar da shirye-shiryen tarukan ranar Quds ta duniya a kasashe daban-daban.

A rahoton da tashar Alalam ta bayar, a kasar Iran an kammala dukkanin shirye-shirye na gudanar da tarukan ranar Quds ta duniya, da hakan ya hada da taruka da jawabai, da kuma jerin gwano a dukkanin biranan kasar.

Haka nan a kasar Iraki, cibiyoyi da kungiyoyi daban-daban suna shirin gudanar da wadannan taruka, kamar yadda haka lamarin yake a kasashen Lebanon, Yemen, da wasu daga cikin kasashen kasashen yankin gabas ta tsakiya.

A nahiyar Afirka ana gudanar da irin wadannan taruka a kasashe da dama, da suka hada da Najeriya, Afirka ta kudu, Kenya, Tanzania, da sauransu.

A kasashen Nahiyar Asia ma akan gudanar da tarukan ranar Quds a kasashe irin Malaysia, Indonesia, India, Pakistan Bangaladash da makamantansu.

Haka ma a wasu kasashen turai, da suka hada da Burtaniya, Canada, Amurka, Austria, Jamus da sauransu.

Marigayi Imam Khomenei ne ya assasa ranar Quds ta duniya a Juma’ar karshe ta kowane watan Ramadan, domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu kan zaluncin da Isra’ila take yi musu, da kuma yin Allawadai da keta alfarmar masallacin Quds mai tsarki da yahudawa suke.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ana Ci Gaba Da Shirye-Shiryen Raya Ranar Quds Ta Duniya A Kasashe Da Dama”