February 8, 2023

Ana ci gaba da kiraye-kiraye ga kasar Amurka, da ta dage takunkuman da ta kakabawa kasar Syria.

Ana ci gaba da kiraye-kiraye ga kasar Amurka, da ta dage takunkuman da ta kakabawa kasar Syria, a gabar da adadin mutanen da girgizar kasa ta hallaka a wasu sassan Türkiyya da Syrian ya haura 6000.
Ya zuwa jiya Talata, adadin wadanda suka rasa rayukan su sakamakon mummunar girgizar kasa 2 da ta aukawa Türkiyya ya kai mutum 5,434, yayin da a Syria adadin ya kai mutum 812.
Yayin da ake ta hankoron ganin an samar da damar ayyukan ceto a yankunan da ibtila’in ya shafa a Syria, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta soki lamirin takunkuman da Amurka ta kakabawa kasar, tana mai cewa, takunkuman sun dakile damar shigar jami’an ayyukan jin kai sassan kasar da bala’in girgizar kasar ya lalata.
Cikin wata sanarwa, ma’aikatar harkokin wajen Syria ta ce al’ummar kasar na amfani da hannayen su, da kananan kayayyakin aiki domin hako baraguzan gine-gine da suka danne mutane, kasancewar takunkuman Amurka sun hana shigar da muhimman kayayyakin aiki da ake bukata, domin gudanar da ayyukan ceto yadda ya kamata.
Kazalika sanarwar ta ce al’ummar kasar sun rasa damar samun magunguna, da kayayyakin kiwon lafiya da ake bukata a irin wannan lokaci, don haka suna cikin barazana da yiwuwar kamuwa da cututtuka.
A wani ci gaban kuma, ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta yi kira ga sassan kasa da kasa da su matsawa Amurka lamba, domin ta dade takunkuman da ta kakabawa Syria, ta yadda za a samu zarafin gaggauta shigar da kayayyakin tallafin jin kai na kasa da kasa, zuwa yankunan da girgizar kasa ta shafa ba tare da wata matsala ba.

 

©(Saminu Alhassan)

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Ana ci gaba da kiraye-kiraye ga kasar Amurka, da ta dage takunkuman da ta kakabawa kasar Syria.”