Ana Ci Gaba Da Gwabza Fada A Sudan

Rahotanni daga Sudan na cewa an yi ta harbe harbe da jin fashewar abubuwa a fadin birnin Khartoum a rana ta 20 a jere da barkewar rikicin.
An kuma samu tashin bama-bamai a garuruwan Omdurman da Bihar da ke makwabtaka da su.
Sojoji dai a kasar sun ce a shirye suke da su bi sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta kwanaki bakwai.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a tsakanin sojojin da kuma dakarun kai daukin gaggawa na RSF.
Bayanai sun ce ana kokarin korar dakarun RSF daga yankin da ke kusa da fadar shugaban kasa da kuma hedkwatar sojoji.
A halin da ake ci dai jama’a na ci gaba da ficewa daga kasar a daidai lokacin da bayanai ke cewa babu alamun kawo karshen fadan a nan kusa.
Babban sakataren MDD, Antonio Guteress, ya bukaci janar janar din dake rikici a Sudan, dasu dakatar da fadan, su kuma dauki dukkan matakan da suka dace na sanya maradun al’ummar kasar a sahun gaba.