An zartar da hukuncin kisa kan Alireza Akbari, tsohon mataimakin ministan tsaro na Jumhuriyar Musulunci ta Iran kuma babban dan leken asiri na kasar Burania a kasar Iran daga baya a safiyar yau Asabar.

An zartar da hukuncin kissan ne bayan da wata kotun daukaka kara a nan JMI ta tabbatar da hukuncin kisa da wata babban kotu ta yanke masa. Shafin yanar gizo na ma’aikatar sharia a nan kasar Iran Mizan.ir ya bayyana cewa Alireza Akbari dan shekara 61 a duniya, wanda kuma ya taba rike mukamin mataimakin ministan tsaro ya zama babban dan leken asiri gwamnatin kasar Burtaniya daga baya. Inda ya bata asiran gwamnatin JMI wadanda suka shafi tsaron kasa na ciki da wajen kasar.
Tun shekara ta 2019 ne jami’an tsaron kasar Iran suka kama Akbari bayan sun tattara bayanai a kan tafiye-tafiyensa zuwa kasashen waje musamman zuwa kasar Burtania inda yake bada asiran gwamnatin kasar Iran musamman a matsayinsa na tsohon ma’aikacin gwamnati. Kuma kotu ta tabbatar da cewa Akbar ya karbi kudade daga hannun wadanda yakewa aiki wadanda suka hada da Euro 1,805,000, fam 265,000, da kuma dalar Amurka $50,000 don ayyukan leken asiri a sane.
Daga cikin an tabbatar da cewa Akbari ya bawa kasar Burtaniya labara dangane da Shahid Mohsen Fakhrizadeh wanda HKI ta kashe shi a shekara 2020.
Sakaren harkokin wajen Burtania James Cleverly ya bukace gwamnatin JMI ta sallami Akbari kasancewansa dan kasar Burtania ne.