An yi zanga-zangar “Free Palestine” a birnin New York ta kasar Amurka

Rahotanni daga kasar Amurka na nuna cewa dubban masu Zanga-Zanga ne suka fito kan titin birnin New York don nuna goyon bayan samar da ‘yantacciyar kasa ga Falasdinu kana kuma sun nuna rashin amincewa ga cin zali da kasar Isra’ila ke aiwatarka kan Falasdinawa a jiya Juma’a.
Dayawa daga al’ummar Falasdinu ne suka nemi mafaka a yankin kudancin Gaza a yau 14 ga watan Oktoba biyo bayan barazanar da kasar Isra’ila ta yi na kai harin ramuwar gayya kan kasar harin da Hamas suka yi mata wanda ya kasance mafi muni cikin shekaru hamsin.
Masu zanga-zangar dai sun nemi kawo karshen abinda suka ambata da Mamayar Isra’ila a yankin Falasdinu. Zanga zangar ta ja hankali dayawa matasan ke rike sa tutocin kasar falasdinu kana kuma suna neman kasar su ta Amurka da ta janye goyon bayanta ga kasar ta Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya.
Kamar dai yadda kafafen yada labarai suka ruwaito, mayakan Hamas sun kutsa kai zuwa kasar Isra’ila a ranar Asabar din da ta gabata kana kuma sun yi nasarar halaka Yahudawa sama da 1,300.
A hirar da aka yi da Farfesa Zacharia, daya daga mahalarta zanga-zangar ya nuna damuwarsa inda kuma ya bayyana cewa mulkin mallakar da Isra’ila ke nunawa Falsdinawa yakamata ya zo karshe, yanzu. Farfesa Zechariah wanda mahaifinsa ya kasance dan asalin yankin Jerusalem ya ce hakan ba abinda zai cigaba da haifarwa face yaduwar fitina da zaluntar al’ummar Falasdinu.
Mahalartar zanga-zangar dai na rera taken “Daga kogi zuwa teku, Falasdinu zata ‘yantu”
Sai dai kuma wasu yahudawan sun ga taken zanga-zangar a matsayin neman rushe daular yahudu. Amma a bangare guda mahalarta zanga-zangar sun nuna wannan itace daidaito tsakanin kasashen biyu.